Ganduje ya tura wa majalisa kwarya-kwayar kasafin N33.8bn

Bukatar na zuwa a yayin da jihohi suka fara gabatar da kasafinsu na 2022.

Ganduje ya tura wa majalisa kwarya-kwayar kasafin N33.8bn

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya tura wa Majalisar dokokin jihar kwarywa-kwaryar kasafin kudi na Naira biliyan 33.8 domin amincewarta.

Bukatarsa ta kwarya-kwaryar kasafin kudi a kan wanda aka yi na sheakrar 2021 na zuwa ne a daidai ranar da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gabatar da kasafin kudin jiharsa na 2022 na Naira biliyan 233.

Tun a makon jiya ne dai Shugaba Buhari ya gabatar wa Majalisar Tarayya daftarin kasafin kudin 2022 na Naira tiriliyan 16.39.

Takardar da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hamisu Chidari, ya karanta a zamanta na ranar Talata ta ce kwarya-kwaryar kasafin ya kunshi biliyan  N21.5 na manyan ayyuka, biliyan N9.2 na gudanar da ofisoshin gwamnati da kuma biliyan N3.22 na biyan albashi.

Takardar ta ce idan aka sanya kwarywa-kwarywar kasafin kudi da aka gabatar a cikin kasafin 2021 na Jihar Kano, jumullarsa zai karu zuwa Naira biliyan  231.7.

A cewar gwamnan, yin karin kasafin ya zama wajibi domin gwamnatin jihar ta samu damar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta da kuma kammala manyan ayyuka da ta faro.

Ya ce za a samo kudaden ne daga harajin da gwamnatin jihar take tarawa da kuma wasu hanyoyi da ta bullo da su.

Tuni dai majalisar ta amince da kudurin domin ci gaba da aiki a kai a zamanta na gaba.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno