Ganduje ya yi alkawarin baiwa nakasassu ilimi kyauta

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shirinsa na baiwa nakasassun jihar ilimi kyauta. Gwamnan ya bayyana hakan yau lokacin da yake jawabin bikin rantsar da shi, a matsayin Gwamnan jihar karo na biyu. Ya kuma yi alkawarin baiwa ‘yan makarantun firamaren jihar ilimi kyauta. Gwamna Ganduje, ya ce za a yi wa […]

Ganduje ya yi alkawarin baiwa nakasassu ilimi kyauta

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shirinsa na baiwa nakasassun jihar ilimi kyauta.

Gwamnan ya bayyana hakan yau lokacin da yake jawabin bikin rantsar da shi, a matsayin Gwamnan jihar karo na biyu. Ya kuma yi alkawarin baiwa ‘yan makarantun firamaren jihar ilimi kyauta.

Gwamna Ganduje, ya ce za a yi wa daliban jihar sassauci da ke karatu a manyan makarantun jihar, kuma zai dora daga cikin ayyuka  ci gaba da ya soma a karo na farko, a fannin ilimi, noma, kiwon lafiya da dai sauransu.