Ganduje ya yi wa fursunoni 90 afuwa
Gwamnan ya yi alkawarin sakin karin fursunoni nan da kwanan 70, wato lokacin Babbar Sallah
Gwamann Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya yi afuwa ga fursunoni 100 a ci gaba da bukukuwan Karamar Sallah a jihar.
Ganduje ya yi musu afuwa ne a yayin ziyarar Sallah da ya jagoranci ’yan Majalisar Zartarwar Jihar Kano tare da shugabannin siyasa da wasu manyan mutane zuwa Gidan Yarin Goron Dutse a ranar Litinin.
- MDD ta yi alkawarin taimaka wa Borno kawo karshen Boko Haram
- DAGA LARABA: Anya Ta’addancin ’Yan Bindiga Zai Zama Tarihi A Najeriya?
Gwamnan ya yi alkawarin “Sakin karin fursunonin nan da kwanan 70, wato lokacin Babbar Sallah,” yana mai umartar wadanda aka sallama da su je gwamnati ta yi musu rajista domin koyon sana’o’in dogaro da kansu.
Sanarwar da kakakin gwamnan, Abba Anwar, ya firtar ta bayyana cewa dalilan yi wa fursunonin afuwa sun hada da: “Rashin lafiya da tsufa da kuma rashin iya biyan tarar da kotu ta yi musu; Har da wadanda aka yanke wa hukuncin kisa.
“Duk da cewa wadansunku an riga an koya musu sana’o’i, masu son samun karin horo su je su yi rajista da gwamnati domin samun wani horo kan sana’o’in dogaro da kai.”
Gwamnan ya bayyana cewa an yi musu afuwa ne domin ba su dama su gyara halayyarsu su zama mutane nagari, gami da rage cunkoso a gidajen yari.