Ganduje zai ciwo bashin Naira biliyan 20
Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya aike da takarda ga Majalisar Dokokin Jihar yana neman amincewarta don ya ciwo bashin Naira biliyan 20 daga Babban Bankin Najeriya (CBN) domin gudanar da wasu aikace-aikace a jihar.Da yake karanta wasikar a zauren majalisar, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Alhaji Yusuf Abdullahi Ata, ya ce gwamnatin […]
Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya aike da takarda ga Majalisar Dokokin Jihar yana neman amincewarta don ya ciwo bashin Naira biliyan 20 daga Babban Bankin Najeriya (CBN) domin gudanar da wasu aikace-aikace a jihar.
Da yake karanta wasikar a zauren majalisar, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Alhaji Yusuf Abdullahi Ata, ya ce gwamnatin jihar tana bukatar wannan kudi ne domin gudanar da wasu ayyuka kuma daga cikin adadin kudin za a bai wa kananan hukumomi Naira biliyan shida a matsayin rance da za su biya cikin shekara 20.
Ya kara da cewa sannan gwamnati za ta sallami ’yan fensho da biyan albashin sababbin ma’aikatan tsabta da aka dauka da aiwatar da batun ciyar da ma’aikata gaba da sauran abubuwan inganta rayuwar al’ummar jihar ta Kano. Daga karshe, Mataimakin Shugaban Majalisar Alhaji Hamisu Chidari ya bukaci kwamitin da aka dora wa alhakin duba bukatar ya gaggauta ba da rahoto bisa yin la’akari da muhimmancin al’amarin.