Ganduje zai tantance jam’iyyu kafin kamfe a filin wasa na Sani Abacha

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce daga yanzu sai jami’an tsaro sun tantance duk jam’iyyar da ke son amfani da filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata don yakin neman zabenta. Gwamnan, a wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Muhammad Garba ya fitar ranar Litinin, cewa wannan matakin ya biyo bayan […]

Ganduje zai tantance jam’iyyu kafin kamfe a filin wasa na Sani Abacha

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce daga yanzu sai jami’an tsaro sun tantance duk jam’iyyar da ke son amfani da filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata don yakin neman zabenta.

Gwamnan, a wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Muhammad Garba ya fitar ranar Litinin, cewa wannan matakin ya biyo bayan kokarin gwamnatin na bai wa dukkanin jam’iyyu dama iri daya, ba tare da nuna bambamci ba.

Ganduje ya ce baya ga filin wasan, duk wasu kayayyakin yakin neman zaben da ke karkashin ikon gwamnati a bude suke ga jam’iyyu don babban zaben 2023.

“Jam’iyyar APC a Kano ta yi imanin a matsayinsu na ’yan kasa, ’yan adawa na da hakkin yin amfani da dukiyar al’umma wacce su ma tasu ce, wajen gudanar da yakin neman zabe,” inji shi.