Gangamin tsabtace muhalli a Ibadan zai hada da mabarata
daruruwan maza da mata masu yawon bara a kan hanyoyi da masu tabin hankali suna daga cikin na farko da Gwamnatin Jihar Oyo ta ce za ta fara kawar da su daga kan titi domin tabbatar da fara aiki da dokar tsabtace muhalli da aka fara a Ibadan a makon jiya. Da yake yi wa […]
daruruwan maza da mata masu yawon bara a kan hanyoyi da masu tabin hankali suna daga cikin na farko da Gwamnatin Jihar Oyo ta ce za ta fara kawar da su daga kan titi domin tabbatar da fara aiki da dokar tsabtace muhalli da aka fara a Ibadan a makon jiya.
Da yake yi wa Aminiya bayani, Kwamishinan Muhalli na Jihar Oyo, Cif Isaac Ishola ya ce gwamnati ta kafa kwamitin tabbatar da wannan aiki mai wakilai 12 a karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikata, Dokta Gbade Ojo. Ya ce a makon gobe ne kwamitin zai fara aiki gadan-gadan domin kawar da mabarata da masu tabin hankali daga kan titunan birnin Ibadan.
Ya ce manyan jami’an gwamnati da suka hada da kwamishinoni da masu bayar da shawara ga Gwamna da likitoci da jami’an duba gari da askarawan Yes-O, su ne aka raba su kashi-kashi domin ziyartar manyan kasuwannin Ibadan, inda suka yi wa ’yan kasuwa bayani a kan dokar hana cinikin kaya a kan titi da dokar tsabtace muhalli wacce za ta shiga gidan kowa.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa kimanin kashi 75 zuwa 80 na mutane da suke yawon barace-barace a kan titi a Ibadan, sun fito ne daga Arewa, inda ake ganin maza tsofaffi da matasa da babu wata nakasa a jikinsu da tsofaffin mata rike da kananan yara suna yawon bara. Ba safai ake ganin masu nakasa a kan hanyoyi ba kuma babu kananan yara ’yan makarantar allo a cikin irin wannan yawon bara.
Kwamishinan ya ja kunnen wadannan mutane da babu nakasa a jikinsu amma suke yawon bara, kan su hanzarta komawa garuruwansu na asali ko doka ta hau kansu. Ya ce suna iya shiga cikin ’yan uwansu wadanda nakasassu ne da gwamnati ta killace su a wani sansanin da suke zaune a Ibadan.