Gangancin gunjin Gurarar Goronyon gwauro

Gada-gadar ganganci Gunjin gabotaranci Gangarowar gwauranci Gura-gurar Gurarar garanci Gardamar gaulanci   Tulun tuttulewa Tamburan tabarbarewa Tafkin tunzurowa Tarzomar turo ruwa Tarawar tarwatsewa   Guga Gumurzun ganga Garewani ganga-ganga Gulbin gudun guga Garnakakin gwauron gwagware gagga-gagga   Burtsowar burtsatse Kwararowar kwakware a kimtse Rangajin rijiya a rumurmutse Kwaramniyar kutunguila ta kwamtse Hake-hake a hargitse   […]

Gangancin gunjin Gurarar Goronyon gwauro

Gada-gadar ganganci

Gunjin gabotaranci

Gangarowar gwauranci

Gura-gurar Gurarar garanci

Gardamar gaulanci

 

Tulun tuttulewa

Tamburan tabarbarewa

Tafkin tunzurowa

Tarzomar turo ruwa

Tarawar tarwatsewa

 

Guga

Gumurzun ganga

Garewani ganga-ganga

Gulbin gudun guga

Garnakakin gwauron gwagware gagga-gagga

 

Burtsowar burtsatse

Kwararowar kwakware a kimtse

Rangajin rijiya a rumurmutse

Kwaramniyar kutunguila ta kwamtse

Hake-hake a hargitse

 

Tambarin tururuwa

Gauden Guden galatsin gantsarewa

Kafin-cirin kwalfewa

Taga-tagar Tigar tangazowa

Gadarar ga-ruwa

 

Babbar bulkarar Bakalori

Budin bakin Bahari

Basirar busharar Bashari

Burgar buga-bugar Bukari

Batun bututun butar bayan-gari

 

Bahaushe na dauri

Yana bankar bauri

Ya san mai kokari

Ya fasko mayaudari

Babbar aika-aika na da hadari

 

Torokon tumbatsar tafki

Tulluwar tundurki

Turnukun tuwon tuki

Takun tattaki

Turka-turkar tumaki

 

Kwarar kududdufi

kundunbalar kamun kifi

karajin sukar kaifi

darkakin dumfarar dafi

Adon-gari a yafa mayafi

 

Salalar salka

Sake-saken suka

Saukowar samari sululu sakaka

Sambatun surutun sakatar sambarka

Satun sumunin sauka

 

Marka-marka

Tuttudowar tafka-tafka

Bambamin barka

Babatun baraka

Fafutikar fafatawar fuffuka

 

An ci tuwo an koshi

Ba ruwan jika makoshi

Al’umma na biyar bashi

Lamarin na da ban haushi

An kika bayan kai toshi

 

In an rasa ruwan wanka

Rani, damina da kaka

Sai ai ta haka kwakware

Dan-garuwa yai ta kwanare

A duba biranen karkarar bukka

 

Baban-burin-huriyya

Gwauro yai kwakyariya

Birnin an yi malalen rariya

Talakawa sun yi juriya

Matsaloli na dada yi wa kasa kawanya

 

Tabawa ranar samun da ta rare aguje, na ga GADARAR GADA-GADAR GANGANCIN GUNJIN GURA-GURAR GURARAR GORONYON GWAURON GORAR-YOYO da BAMBAMIN BULKALAR BARAGADAR BURGAR BILINBITUWAR BADAKALAR BULBULOWAR BUTOCIN BAJINTAR BAKALORI da  ZUGA-ZUGIN ZABUROWAR ZABARIN ZUGAR ZUBAR ZOBE, TAMFAR TOROKON TULLUWAR TULUN TOLATSEWAR TUTTULOWAR TUMBATSAR TURNUKUN TUFKAR TAFKEKEN TAFKIN TEKU, kai ko dai in ce GIRGIJEN GAJIMAREN GAFTAROWA; sai SHA’ANIN SHAWARAR SHA’AWAR SHIRIRITAR SHIRMEN SHASHANCIN SHIRYA SHIRORO; KAKARIN KAYAN INJI; da KIRINIYAR KIN JI,  duk dai a tsaunin gwagware da ke binin Dabo, inda ba a dabo, domin bututun bezar baza ruwan  birnin da kewaye ta yi ta tumbatsa tana kwararewa, amma al’umma babu ko dis da ke diga a farfajiyar gidaje, ballantana a samu na dauraye tufafi da sole jiki da sabulu, har ma bayan an ci tuwo an tauna tantakwashi, an koshi a samu na jika makoshi.

Yayin da jallon jiga jikin jama’a ya tsiyaye ya kwaranye, sannan ya malaye male-male, al’umma sai baza na-mujiya suke yi, suna ta kalle-kalle, har na ji wani ya koka cewa, ’yan ga-ruwa na cin kasuwa, tunda yau jarkokin da za ka saya a Hauro dari kofar hanci ba za su wadatar ba.” Ni kuwa ina ta so in nusar da Malam mai Koke cewa ai tuni Majalisar Mulkin Ministocin Baban-burin-huriyya ta yunkuro wajen yi wa tufkar hanci, amma dai na ja bakina alaikum.

Tun cikin watan Marisar bana dai na ji Gwamnatin Baban-burin-huriyya ta bijiro da batun kashe kudin Farin-sa, har yayyafin yuron yakice  matsalar ruwa a birni da kewayen Jihar Tumbin giwa, da na ga kwarar kududdufi sai na dauka aikin Baba ne aka fara, har na so in ce bari kawai mutum ya yi kundunbalar kamun kifi.

’Yan makaranta ko dai in yasar da BUTU-BUTUN BURUNTUN BABATUN BATAN-BAKA-TAN-TAN? Ka da dai ku ce kun gaji da gafara nan a koro bujimi, amma ba ku ga kaho ba.

Haurobiyawa, al’ummar birnin Dabo, inda ba a dabo suna ta kwallara kuka wai sun yi DODAR, sun sha DUNDU DAHIR, har ta kai ga suna dari-darin dar-dar; wai sun yi SAK, amma sun yi CAK. Karshen dai TIKA-TIKA TIK. Masu kokawa lallai akwai babbar bukatar tunkarar Gwamna gwarangwam Gandun Aiki, don jin yadda zai tunkari wannan muhimmin gagarumin aiki; sai Wakilan Rafkiya da Sani-Atta, a jiwo mana irin tanadin dokokin dukan tsilli-tsillin matsalolin al’umma da suke yi.

A daina bijiro mana irin wannan SUKA-DA-BURTSATSEN MAGANGANU a makarantar nan, matukar dai ba so ake yi in yi ta tafkar masu koyon watsattsake da fallen shafukan mujallu da makalu da jaridu da wagagen littattafai ba. Don haka kuna da zabi, ko dai KU YI NA JAKI, ko KU CI NA JAKI. Kai mu yasar da DAKON DAKON MANGALAR AURA.

Da zarar an jiwo ta bakin mahukunta, idan har batunsu bai gamsar ba, sai kawai kowa ya bayar da himma wajen tonar kwakware. Dama can akwai KWAKWAREN LEMO da KWAKWAREN ZAKI a birnin Dabo, ba sai kawai a kai butoci a ciko su taf ba?

Wai shin Dodon dodanniyar dumuiniyar dundumin Dodorido, Direban allin makarantar Dodorido da ke cikin farfajiyar Amintacciyar Jaridar kasar Haurobiya, mene ya sha maka kurungu da wannan matsalar, kai ba Mai martaba Masanin Sisi-da-sisi ba; ba Gwamna gwarangwam na gundumar gandun aiki ba; sai shiga sharo ba bujimi da karsana ko? Kai haka ne fa, ni ma dai fargabata, ka da magabta su yi mini lakabin HAZIKIN HARZUKA HARGOWAR HAYAGAGAR HUTSUN HAUTSININ HAYANIYAR HANYAR  HARAMBEN HARIGIDON HAURUBJA!

Mutanen birnin Dabo dai, kirana, shi ne, ka da ku bari a yi muku dabo, ko WALA-WALAR WALWALIN WALIYON MASHILLARAR WALKIYA. Domin sakarcin sakacin sagaraftun solobiyon sulun sululunku zai iya sanyawa al’ummar Birnin Lawurje su yi muku dararraku hahaha!

To haka lamarin yake, tun da tuni aka ruwaito yadda Gwamna gwarangwam na Jihar Bayan-Kada Malam Nasara el-Rusau ya shawo kan matsalar. Kai yaushe rabon ma da ku ji mutanen birnin Lawurje sun koka, ta yiwu a ce tun daga zamanin Gwamnan nan Kakkarfa dan garin masu rake; ko Malam Namando, wanda a makarantar nan muka fasko cewa bai san bihim ba.

Arewatawan birnin Dabo ka da fa ku yi ta tutiyar cewa, Dodon dodanniyar dumuiniyar dundumin Dodorido ya dora wa mahukunta laifi kan rashin yin katabus, har ku je kuna ta kus-kus, a je a karke da kurmusun kamusu, wai wasu kalaman kalallame kalmomi da ake kira JAMUS A KAMUS. Batun ingarman karafunan titin tarragon layin kwangirin dogo, ba tare da tsahirtawar laulayin wulwulawar hannayen agogo ba, wannan dadadden birni an dade ana yi masa kirari, wato ta Dabo ci gari, ko da me ka zo an fi ka. Kun ga ke nan wannan bai rasa nasaba da cewa talalar talaucin talakawanku ya zarta na manyan biranen kasar nan; haka dimbin daukin dawainiyar dago daidaikunku da albarkar arzikinku ya yi kasurar da ta dara na saura. Bisa la’akari da wannan lallai sai a lalubo bakin zaren, wato a duba a ga ni, ni da ke da kai da ku da su, har ma da wasunmu wane irin yunkuri muke yi wajen warware awarwaron wahalhalu ko sunce sasarin sargafe al’umma?

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos