Gangankon gwangwanin garewanin gahawa
Mai shayin Haurobiyawa Shi ke tuttule tulun ruwa Ya a za sanwa Murhu yai ta tafarfasa garwa Mun kwankwadi ruwan bunu Asirin magabta ya tonu Sun hana kasa ta ginu Komai sun sa hannu Jama’a na ta maganganu Shan koko bukatar rai Kandamar kunu ma sarai Surbar shayi sai dankwarai Wa-ka-ci-ka-ta-shin wasarairai […]
Mai shayin Haurobiyawa
Shi ke tuttule tulun ruwa
Ya a za sanwa
Murhu yai ta tafarfasa garwa
Mun kwankwadi ruwan bunu
Asirin magabta ya tonu
Sun hana kasa ta ginu
Komai sun sa hannu
Jama’a na ta maganganu
Shan koko bukatar rai
Kandamar kunu ma sarai
Surbar shayi sai dankwarai
Wa-ka-ci-ka-ta-shin wasarairai
Ban da tsokanar sakarai
Kun ji ta’adar Larabawa
Turka-turkar Turawa
Tattakin takun Turkawa
Majigin maganadisun Mekzikawa
Artabun arangamar Arewatawa
Kowa dai ya gyara
Sai shirin ya zam sharbar gara
Mu tattaru kowa ya hallara
Mu daina kwado da dara
Kayan shaye-shaye su bar shuhura
Haure-hauren hauragiya
Hargagin hatsaniya
Hayagagar hawainiya
Hautsinin hayya-hayya
Hatsabibancin hatsabibiya
Al’umma
Ai fafutikar makoma
Ai aiki kasa da sama
A tattaru kowa ya kama
A yanayin nan ba zama
Garmahon Garbatin gidan Shehi
Girma-girma ganin gashi
Balati ta sha washi
Batun aiki ba fashi
Gwamnati tai tsayin tashi
Ana ta sukar mashi
Mahukunta sun yi yaushi
Haurobiyawa na biyar bashi
An harzukasu sui ta fushi
Maganganunsu iwa Turancin Faranshi
Azargagiyar zargi
Wai Baba yai magagi
Ko ya shige sagagi
Garbati yai firgigi
Ya ce Baba ba wargi
Wannan ne wa’adin karkare zango
A kwanshi gara da zago
Ai kidin gangunan bahago
Mu ga takun amarsu ta ango
Har an fara duba agogo
Kasa ko’ina a hango
Kayayyaki dibge a shago
Wasu ma sun lafke a kango
Ina gizo-gizon dakin gwaggo
Bar dage kafar farin dango
A zaburar da al’umma
Kowa yai kaimin karin himma
Ai kwadon rama
Ai maganin rama
Sai a samu makama
A sake sabon salo
An dai yi jimirin kallo
An ga masu dukan kwallo
Ga masu kwankwadar ruwan jallo
Da masu yi wa jama’a gwalo
Baban-burin-huriyya
Kai tarairayar tariya
Bin kadin lamuran zirya
Ka watsar da kiren karya
Batun ingarman karfe muke a farfajiya
Bayan dawowar Baban-burin-huriyya daga taron tula tattali tuli-tuli na tsurkun tsakiyar tsukukun Gabashin duniya da Arewacin Ifirikiyya, Haurobiyawa sun jefa azargagiyar zargi kan cewa ko Baba ya je jika makoshi ne har ya yi SHELAR SHATALE-TALEN SHANTAKEWAR SHAN SHAYI? Ganin irin martanin da na yi wa masu kulla-kullar zarge-zargen zaren afatati, sai wasu ma ke son su jefa irin wannan zarge-zargen kan cewa ko dai Direban allin makaratar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya ne GARBATIN GIDAN SHEHI, marikin garmahon gangunan gunjin Baba?
Da har zan ce ai ba ni ba ne, sai kawai na ji Garbatin gidan Shehi na ta baza batutuwa ta cikin garmahonsa, cewa Baba ba ya na-kasa, ballantana a kasa, a kwashi kashi, musamman in yana bakin dagar dumuiniyar ayyukan tarairayar Haurobiyawa. Hakika na gamsu da wannan amsa, amma yaya za mu yi da masu yi wa Baba lakabin YAWALE, ko dai suna nufin mai yawan yawon walle-walle; ga shi ya yi shatale-talen shan shayin Larabawa;daga nan ya yi zirya zir zuwa birgimar Birtaniya; daga can zai yi ruju’i ko sai wata nahiyar sararin samamen duniya?
Ko ma dai wadanne irin tsokale-tsokalen tsangwamar tsugudidi tsigarewa za a yi ta yi, na san cewa, ‘zamanin mulkin mulaka’un Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulki, har YAWON-WUNI-WUNI ya jefa masu fuka-fukin tashi,’ inda suka ta cike-ciken caccakar shafukan laluben jari a mashakatar lilo da tsallake-tsallake. Wasu sun dace, sun dafe wasu kuwa na-mujiya ya kafe, tawayar rayuwa ta kyafe su.
Shi ma dai Baba ai bai yi kasa a gwiwa ba, domin ya bullo da AIKIN FAWA, ka da dai a ce an tura masu fuka-fukin tashi garin FAWWA da ke karkashin masarautar birnin Dikko su yi dakon dako. A’a, an dai bullo da dabarbarun laluben na-koko a cikin kowane loko na kasar Haurobiya da zimmar kawar da zaman kashe fatari da gararambar watangaririya mai hadari.
Akwai dimbin alfanun da Baban-burin-huriyya ya lalubo a balaguronsa, musamman lokacin da ya yi shatale-talen shantakewar shan shayin Larabawa, sannan aka kara da birgimar Birtaniyawa. Lamarin dai na bukatar gwagwiyar goribar garhamahon gurmin garayar Garbatin gidan Shehi. Saboda haka lallai a kwankwadi madin modar gahawa.
Gangankon gwangwanin garewanin gahawa na bukatar gangamin gamayyar gwagwagwar gama-garin al’umma don raba shayin da kowa zai kwankwada ya yi hani’an, tun da mun fasko cewa, ‘Sawun-diyyar Larabawa na shirin kafa katafariyar matankadar tunkuza a Haurobiya, ta yadda watakila a dakile azarbabiyar masu ziryar safarar TURAR-MOLO da KOKINO da sauran nau’ukan shaye-shaye da romon birkita kwakwalwar al’umma. Kai ga ma kokarin kasar Katar ya kayatar.
Uwa-uba, a farfajiyar koyon watsattsake da falle shafukan mujallu da makalu da jaridu da wagagen littattafai, mun yi darasin MAHANGAR MAKEKEIYAR MAKARANTAR MAMA, al’amarin da muka ta’allaka da hadin gwiwar Mama da ‘’yan kayataciyar kasar Katar, har ta hada hannu da mutanen Sudan da suka dare a sirdi sadidan. Wannan ne ya sanya Direban allin makarantar nan bai saduda ba, wajen ganin ya tallafa wa Mama ta kafa Babbar bukkar bobon bokokon Baban-burin-huriyya.
Lallai a sake sabon salo, domin an dai yi jimirin kallo, inda tuni aka fasko masu dukan kwallo da masu kwankwadar ruwan jallo; wasu ma suna yi wa jama’a gwalo; ta cikin kurtun magana kawai sai ka ji masu karatun ALLO, suna ta wataya tamkar masu baza bindin bezar TALO-TALO, sai su ce HALO ALALO!
Sannan fadin kasa ko’ina a hango irin kayayyakin da ke dibge a shago, don wasu ma sun lafke a kango dabaibaye da yanar gizo-gizon dakin gwaggo, sun ki daina dage kafar farin dango. Saboda haka sai a zaburar da al’umma, kowa ya yi kaimin karin himma. A zo a yi kwadon rama don maganin rama, ta yadda za a samu makama.
’Yan makaranta mu nusar da Baban-burin-huriyya bukatar kara tarairayar tariya da bin kadin lamuran zirya, sai ya watsar da kiren karya, don batun ingarman karfe muke a farfajiya
Haurobiyawa mu yi wa kanmu masalaha, mu kiyayi harkalla da hakilon shiga wahala, don haka sai a kula ka da a zubar da kwalla. In mun kiyaye, za mu ji dadin dararaku hahaha!