Gangar siyasa ta fara kadawa, zaben 2019 yana karatowa
Wadansu ’ya’yan Jam’iyyar PDP da aka yi kawance da su lokacin zaben 2015 sun fara barin APC mai mulki suna komawa PDP, ya rage wa masu rike da madafan iko tare da wadanda suke amfana da mulkin, musamman wadanda ake cece-ku-ce a kan sun hana kusan kowa ya kusanci Shugaban kasa Muhammadu Buhari, sun makure […]
Wadansu ’ya’yan Jam’iyyar PDP da aka yi kawance da su lokacin zaben 2015 sun fara barin APC mai mulki suna komawa PDP, ya rage wa masu rike da madafan iko tare da wadanda suke amfana da mulkin, musamman wadanda ake cece-ku-ce a kan sun hana kusan kowa ya kusanci Shugaban kasa Muhammadu Buhari, sun makure wuyan fadar Shugaban kasa, sun kankane CBN da NNPC da sauransu, idan suna fatan alheri ga Shugaba Buhari da Najeriya da mutanenta, musamman wadanda aka zalunta, su yi namijin kokari su tsarkake kansu, su gyara tsakaninsu tun kafin lokaci ya kure, wadansu su bi sawu, tarihi ya maimaita kansa irin yadda ta faru da Buhari a 1985. Su dauki matakan neman jama’a su shigo, Gwamnatin Buhari ta kara karfi, maimakon raguwa da kara sukurkucewa, makiya su dada hada kai.
Wadansu sun mutu, wadansu sun rasa lafiyarsu, wadansu sun rasa jarinsu da sana’o’insu da gidajensu. Duk wadannan suna jiran kulawar gwamnati ta biya musu bukatunsu na rayuwa. Tuni suka fara kokawa da gafara Sa, ba su ga kaho ba. Har shi Shugaban kasa Buhari ya yi alkawari da kansa, su yi hakuri za su ga san, kafin ya kamu da lalurar rashin lafiya. Wadanda Buhari ya amince wa suka ci amanarsa da wadanda aka zalunta (tsawon shekaru), har yanzu ba a fara danka wa kowa komai ba daga dukiyar da ake cewa an kwato daga hannun barayin gwamnati, balle su ga irin hukuncin da za a yi wa barayin, sai ma zargin makusanta Shugaban da ake yi da hada baki da wadansu barayin da yaran gungun barayin shugabannin da suke kokarin rusa mulkin na Buhari.
Tilas Shugaban kasa Buhari ya gaggauta yin duk abin da ya kamata domin tunkarar zaben 2019. Ko tsafi aka yi wa Buhari, wadansu makusantansa suke makure gwamnatin tasa sai yadda suka yi, suke hana ruwa gudu, suna dakile duk wani yunkuri na hana sata da zalunci, da kwato duk dukiyar da aka sace mana, suke baje kolinsu suna yin tasu barnar, da hadin kan yaran shugabannin da suka shude, kamar yadda ake ta zargi, har yanzu wadanda ake zargin ba su magantu ba, balle su karyata zargin, Shugaban kasa bai ce komai ba.
Lokaci ya yi da za a karya tsafin, gara a raba Buhari da su tun kafin su raba shi da masoyansa na gaskiya, musamman wadanda aka zalunta, kuma ake ci gaba da zalunta.
Tun da Allah (SWT) Ya jarrabi AnnabawanSa, suka sadaukar da mafiya kusanci da su, kamar mahaifi da da da dan uwan mahaifi a kan rashin yin imani da sakon da Allah Ya aiko Annabawan da shi, babu wani dalili da zai hana Muhammadu Buhari ya sadaukar da kowane ne nasa a kan cin amanar da Allah Ya danka masa ta al’umma. Allah (SWT) da kanSa Ya haramta wa kanSa zalunci, Ya yi umarni mu ma kada mu yi zalunci, Ya ce: “Mafi soyuwa gare Shi shi ne shugaba adali,” mafi rashin soyuwa a wurin Allah shi ne azzalumin Shugaba.
Saboda haka duk mai fatan alheri ga Buhari da ’yan Najeriya ba zai yi amfani da mulkin na Buhari ya yi wata barnar ba, balle KASHE-MU-RABA ko sata, komai kusancinsa da Buhari.
Maimakon a bar su, su halaka shi da mu baki daya, gara a dauki mataki na gaggawa a kansu, shi ne mafi sauki da alheri a gare mu, da a daka ta masu tunanin sai an canja Buhari a kan laifin da ba shi ne ya aikata ba. Allah ba Ya hukunta bawanSa a kan laifin wani makusancinsa (’yan uwa ko iyaye).
Babban aikin da yake gabanmu shi ne, duk yadda za a yi a yi don a canja Majalisar Tattalin Arzikin Kasa da ta kunshi ’yan Kudu zalla, babu ’yan Arewa sam-sam balle Hausa/Fulani. Siyasar ma da ake mulki da ita babu kwamitin balle a yi maganar wakilcin ’yan Arewa a ciki. Duk kasafin kudin kasar ya kare a Kudu-maso-Yamma. Duk wadannan matsalolin ba sa cikin tunanin makusantan Buhari (har da ’yan uwansa) da ake ta korafe-korafe a kansu, abu mafi hadari shi ne da yake su ba ’yan siyasa ba ne, ga al’umma masu kuri’a sun kosa.
Cikakken bincike na adalci ne kadai zai warkar da duk wadansu masu zargi, musamman kowa ya ga an hukunta wadanda zargin ya tabbata a kansu, baicin an kwato mana duk dukiyarmu da suka daka wawaso a kanta, a fara danka wa kowa hakkinsa a hannu. Annabi (SAW) cewa ya yi: “Koda ’yarsa Fadima aka samu ta yi sata, zai sa a yanke mata hannu.” Allah Ya daukaka adalci da adalai, Ya kaskanta zalunci da azzalumai, amin summa amin!
Alhaji Abdulkarim daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN)
Tsohon Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu, Ma’adanai da Ayyukan Gona ta Jihar Kano
(KACCIMA)
Tsohon Shugaban Jam’iyyar Alliance for Democracy (A.D) na kasa.
08023106666, 08060116666.