Gani ga wane…
Duniya ba ta da tabbas, a lokacin da Kanal Mu’amar Gaddafi ya yi juyin mulkin cikin gidan da ba a zubar da jini ba, Sarki Idris da Iyalansa suka tafi gudun hijra a kasar Italiya inda Sarkin ya ci gaba da rayuwa har lokacin da wa’adinsa ya cika. Sabon shugaba ya mayar da matsayinsa daya […]
Duniya ba ta da tabbas, a lokacin da Kanal Mu’amar Gaddafi ya yi juyin mulkin cikin gidan da ba a zubar da jini ba, Sarki Idris da Iyalansa suka tafi gudun hijra a kasar Italiya inda Sarkin ya ci gaba da rayuwa har lokacin da wa’adinsa ya cika. Sabon shugaba ya mayar da matsayinsa daya da kowane dan kasa, ya kan fito ba tare da dogarai ba, wani lokaci a kasa yake yawo ko kan rakumi a cikin kauyuka da dazuzzukan kasar. Ya gabatar da wani koren littafin akidun kasa wanda ya kunshi hakkoki, sharudda da kundin rayuwa a Libiya.
Cikin shekaru kadan matashin ya wa Libiya sabon fasali, angon ya ci angoncinsa, ko wane dan kasa na cin ribar arzikin kasa, ta yadda ko jariri aka haifa a zamanin sai an bashi fili, gida da asusu a bankin kasa, ‘yan kasa ba su biyan kudin wuta ko ruwan sha, wutar da sai a yi shekaru ba ta kifta ba, wasu tun da aka haife su ba su taba ganin duhu ba!
Shugabanci a kasashen Larabawa ba ya zama daidai sai da babbar sanda, inda Gaddafi ya dauko sandar karfe, ya yi amfani da karfin ikonsa wajen ladabtar da duk wanda ya nemi kwance masa rawani. Ya goyi bayan masu neman ‘yanci irinsu Afirka ta Kudu da Palasdinu. Sai da Nelson Mandela ya yaba masa a matsayin wanda ya taimake su a lokacin da kowa ya masu rowa. A cikin gida ya tsare fadarsa, inda ‘Ya’yansa suka sami mukaman Yarima da Ministocin wassani, kuma suka zaburar da ‘yan kasa kan dole a yi nasara!
A lokacin da ya kai ganiyarsa har sadaka ga Almajirai, zakkah ga Mabukatan kasashe da Malamai, kai har Jami’o’i da Massalatai ya rika ginawa a kasashen Afirka, ya kulla aminta ta musamman da Marigayi Sheikh Nasiru Kabara, sannan amini ne ga Marigayi Isiyaku Rabi’u, kai ko yau ka je Bauci sai ka ji ana masa addu’a a gidan Sheikh Dahiru Bauci.
Idan an ce Gaddafi cuta ne, zan iya cewa Gaddafi magani ne, ya mayar da hamada kasar noma ya jawo ruwa, ya taimaka wajen bunkasa noma. Ya zamanantar da kasar da ya gada. Ba ya da gidajen kansa, ko asusu a wasu kasashe. Bai ci shi kadai ba, ya bunkasa tattalin arzikin kasarsa.
Duk da haka Libiyawa suna da daruruwan dalilan kifar da gwamnatinsa, musamman ganin abin da ya faru a Tunusiya da Masar. A lokacin guguwar Larabawa da ta tafi da wasu shugabanni, a ganinsu an take hakkokin da aka yi masu alkawali, inda suke zuwa Masar don shakatawa suna ganin yadda ake. Shugabansu ya wuce shekaru takwas, matasa ba su san kowa ba sai sarki daya, Gaddafi!. Inda aka fara fito musu ta fuskar kabilanci, aka zaburo da ‘yan Al-Bayda, Bengazi, Misrata da Tabruk, daga zanga-zanga aka koma kare kai, aka rika wa doka da oda karan tsaye. Jami’an tsaro suka fara wa kabilunsu biyayya, kowa ya yi ta kansa.
Turawa a karkashin NATO tare da goyon bayan MDD suka shigo da jiragen sama inda suka tabbatar da sun lalata duk filayen jirgen saman kasar, gadoji da na’urorin sadarwa. Faransa ta fito fili ta nuna goyon baya ga ‘Yan tawaye. Inda masu zaman kashe wando suka dauki makamai, Manoma suka dauki bindigogi, kasa ta tarnake da nakiya, wasu fataken suka sulale da makamai inda aka saida wa makiyaya da manoma da arha wasu ma aka basu kyautar mai jigida da tukwicin mai carbi.
Ganin babu sarki sai Allah, Gaddafi ya yi fitar dare a wani gungun motoci daga nan aka bi motocin, jiragen saman NATO suka bude masu wuta, inda ya shige daji, aka shiga nemansa sai can daga bisani wasu suka hango shi a wata kwata, aka zakulo shi daga ramin da yake a boye.
Cikin rikicin an kashe daruruwan ‘yan kasa, yayin da MDD ta nemi a tsagaita wuta don ana kashe talakawa, sai NATO ta nuna dole ta kammala yakin da ta fara, a daidai lokacin da Amurka ta bada gudummuwa ta hannun NATO kuma kasar Katar ta bada filayen jiragen samanta don kai wa Libiya hari. Bayan an ruguza kasar sai Gaddafi ya zama shi ne saitin jiragen sama da bindigogi kowane dan tawaye.
Dikteton da ya raya dimokuradiyya, ya yi shekaru arba’in da biyu yana kan karagar mulki. An rusa ginin da ya gina! A 1969 ya kawo karshen masarauta, zuwa 2011 ya shiga cikin jerin shugabannin da guguwar matasa suka kora, kuma aka kashe a wulakance!
Wani abu da ya jawo masa bakin jini a wajen Turawa shi ne bayani kan faduwar jirgi a Lokabi, wanda wani Balibiye ya amince shi ya kai harin kuma gwamnatin Biritaniya ta nuna abin ba zai yiwu ba sai da sani da izinin shugaba Gaddafi. Inda aka matsawa Gaddafi sai da ya biya kudin diyya na miliyoyin daloli. Sannan ana zargin gwamnatinsa da yin kisan kare dangi a kurkukun Abu Salim, wannan ya sa da aka fara fadan karshe a Libiya tsakaninsa da ‘yan kasa har sai da Turawa a Irelan suka taya Libiyawa da yin bore da jerin gwanon kin gwamnatin Gaddafi.
Libiya ba za ta koma yadda take ba, a yau ana dauke wuta a Tarabulus, wasu garuruwan ma ba haske baki daya, ilmi ya tsaya an mayar da Makarantu gidajen ‘yan gudun hijira wasu makarantun ma har yanzu ba a bude su ba, an ruguza Asibitoci, balle uwa uba tsaro inda kowa ya dauki makami, Maharba na harbi Mafarauta da ‘yan ta’adda sun watsu ko’ina kowa hannunsa nakan kunama! Fyade da tsakar rana, kana kan tituna sai wani ya leko ya harbe ka, ba a fitowa kasuwa, Shaguna a garkame, Bankuna sun zama mabuyar karnuka ko Makewaya.
Haka dalibai masu jarrabawa suna ji suna gani suka bar karatunsu, wasu tun daga wancan lokacin ba su kara karatu ba, ‘yan kasashen waje haka suka baro kasar ba shiri. Babu motocin haya ko acaba, da an ga bako sai a buya idan na harbewa ne a harbe, idan na magana ne a kamo shi sai a yi zancen da za a yi wani lokacin sai an masa kwace. Ko kanikawa, kafintoci da latirishan tare da sauran masu kananan sana’o’i kamar Mahauta, Teloli, Masu wanki da guga da suke zuwa ci rani, duk sun koma kasashensu.
Ganin ra’ayoyinsa sun ci karo da na Turawan Yamma dama ya taba yin zage-zage da Masarautar Saudiya, inda ya nuna wa Sarkin Saudiya yatsa, ya kuma kira su wawaye karunkan Turawa, daga nan aka kulla sai an ga karshensa, bugu da kari ya na neman kawo sauyi a bangaren tattalin arzikin kasashe masu man fetur ta yadda zai bada tubulan gwal na kasarsa a mayar da su sulalla daga nan su zama kudin cinkin mai sabanin dalar Amurka!
Babban abin takaicin shi ne gugguwar Larabawa ta ci gaba da cin kasashe inda kasa kan rushe kamar yadda Bagadaza, Siriya da Yamen suka daidaita. Daga rayayyar kasa ta koma matacciya, komai ya tsaya ‘yan kasa sun zama ‘yan gudun hijira da bakin haure a makwafta, ko su tsallaka Turai inda ake yi masu gori da zagin kare dangi.
A safiya 12 ga watan Oktoba 2011 rayuwar Gaddafi ta zo karshe. A halin yanzu wasu kabilu sun koma farauta da neman damar da za su ci mutumcin wasu kabilu ko wadanda suka samu a tsohuwar gwamnati, amma abin tambaya shi ne, me ya sa matasan suke son ganin bayan ‘yan uwansu, tabbas a lokacin da Gaddafi ya fara tsufa kowa ya fara yin abin da ya ga dama farawa daga cikin iyalensa har zuwa duk wasu ma’aikatan hukuma, aka rika take hakkokin bil-Adama da cin hanci da rashawa, yanzu damar daukar fansa ta samu, ga karancin hakuri, sai hakuri da karin hakuri.
Tabbas gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah. Kasashe sun fadi, kasashe na faduwa, ya kamata kasashe irinsu Sudan su yi wa kansu karatun ta natsu domin su tsira kar su koma baya kamar kasashen da suka daidaita, kamar Libiya kasar da ta yi suna wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali. A ranar da aka kashe Gaddafi, Sakateriyar kasashen waje ta Amurka fitowa ta yi tana dariya tana cewa mun zo, mun yi nasara kuma mun kashe shi!
Ko an so ko an ki Gaddafi ya kawo ci gaba a Libiya fiye da yadda ya iske ta. Ko a lokacin da aka yi masa tawaye an sami wadanda suka shiga gaba wajen bashi kariya, ko gwamna ya yi shekaru hudu sai ya sami ’yan gani kashe ni, balle wanda ya yi shekaru arba’in akan karagar mulki. Tun bayan wafatinsa ba a kara maganar wani abu ba kamar Haddadiyar Daular Afirka (USA) ta yadda za a gina jiragen kasa da hanyoyi a cire iyakoki, fasfo da haraji tsakanin kasashen nahiyar Afirka.
Zaman lafiya ya fi komai, tun bayan tunbuke shi, an gaza samun zaman lafiya a Libiya, kashe-kashe sun zama ruwa dare, an gaza samun hukuma daya da zata jagoranci kasar, a yau wani abu mai kama da yakin basasa ya barke a Libiya.
Mafita ga Libiya da kasashen Larabawa ita ce a koma kundin Al-Kur’ani wanda ya ce, mutane ‘yan uwa ne, a yi sulhu tsakanin juna, mu ji tsoron Allah don mu rabauta. A tarbiyantar da manyan gobe, a kimanta magabata a cire kiyayya ta hanyar yafiya da son juna a ci a sha tare, a zauna a inuwa daya!
Buhari Daure
Abbasiyya, Masar.