Hotunan kadan daga cikin abubuwan da suka faruwa a wannan mako mai karewa
Daga cikin abubuwan da suka faru a wannan makon mai karewa akwai shagulgulan da aka gudanar na Babbar Sallah – da ma wadanda suka gabace ta ko suka biyo baya.
Ga kuma tsallake rijiya da baya da wani matukin jirgin saman yaki na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ya yi a lokacin da ‘yan bindiga suka kakkabo jirgin da yake ja.
Ga kadan daga cikin abubuwan da suka faru a cikin hotuna.
Shugaba Muhammadu yayin da yake takawa a kasa zuwa gida bayan Sallar Idi a Daura, Jihar Katsina (Hoto: Bashir Ahmad)
Dubban Musulmi ne suka halarci Sallar Idi a Babban Masallacin Idi na Ali Kazaure da ke Jos, babban birnin Jihar Filato (Hoto: Hussaini Isa)
Babban Limamin Owerri, babban birnin Jihar Imo, Alhaji Suleiman Njoku, a lokacin da yake jagorantar dimbin Musulmin da suka halarci Sallar Idi (Hoto: Jude Aguguo Owuamanam)
Musulmi na jira a tayar da sallah ranar Idin Babbar Sallah a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba (Hoto: Musa Kutama – Tsohon hoto)
A Mararraba, Jihar Nasarawa, mai makwabtaka da Yankin Babban Birnin Tarayya ma, dimbin Musulmi sun halarci Sallar Idi (Hoto: Ikechukwu Ibe)
Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Honorabul Femi Gbajabiamila yana yanka ragon layyarsa ranar Sallah (Hoto: Ofishin Yada Labarai na Shugaban Majalisar Wakilai)
Yadda aka kyafe raguna gabanin gasa su a al’adar nan da Sakkwatawa ke kira “tareni”. A bisa wannan al’ada akan tara ragunan jama’ar unguwa a wuri daya a gasa (Hoto: Nasir Bello)
A Gombe, raguna sun yi karanci sun kuma yi tsada gabanin Babbar Sallah saboda, a cewar ‘yan kasuwa, abincin dabbobi ya yi tsada (Hoto: Rabilu Abubakar)
A daidai lokacin da ake bukukuwan Babbar Sallah, Masarautar Daura ta nada dan Shugaba Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, a matsayin Talban Daura. A nan Shugaba Buharin ne tare da dansa Yusuf da kuma dan yarsa. Dan Madamin Daura Musa Haro (Hoto: Bashir Ahmad)
Daruruwan Yamanawa sun taru a Taez, birni na uku mafi girma a kasar Yemen, don ci gaba da shagulgulan Sallah ranar Laraba 21 ga watan Yuli (Hoto: Ahmad Al-Basha / AFP)
Jami’an tsaron Afghanistan bayan harin bom da aka kai a safiyar Babbar Sallah gabanin jawabin Shugaban Kasar. Rugugin hare-haren rokoki ya girgiza yankin da Fadar Shugaban Kasar a daidai lokacin da yake shirin gabatar da jawabinsa na ranar sallah. (Hoto by Hoshang Hashimi/AFP).
Filait Laftanar Abayomi Dairo, matukin jirgin saman yakin da ‘yan bindiga suka kakkabo, tare da Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya Isiaka Oladayo Amao. Ranar Lahadi 18 ga watan Yuli Dairo ya tsallake rijiya da baya lokacin da aka harbo jirgin saman yakin da yake ciki a Jihar Zamfara (Hoto: Idowu Isamotu)
Wata ambaliyar ruwa ta mamaye wasu titunan Legas
Bana aikin Hajji ya zo da sabon tarihi inda a karon farko alhazai mata suka sauke farali ba tare da muharrami ba a aikin Hajji na biyu a lokacin COVID-19. An kuma kammala aikin ba tare da wani alhaji ya kamu da cutar ba. (Hoto: Haramain Sharifain).
Wani bawan Allah da ‘yan bindiga suka harba lokacin da suka kai hari a wani yanki na Masarautar Zazzau. A yayin harin dai ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mata masu juna biyu da ma masu shayarwa (Hoto: Aliyu Babankarfi)
Shugaban rikon Kasar Malin, Kanar Assimi Goita a lokacin da yake halartar sallar idi a Babban Masallaci da ke birnin Bamako, inda wani mutum ya yi yunkurin caka masa wuka. (Hoto: AFP).
Wasu daga cikin mutane 150 da gawurtaccen dan bindigar Zamfara, Turji ya sako bayan an daidaita da shi hukuma ta saki mahaifinsa da ta kama. (Tsohon Hoto: Shehu Umar).