Gani ya Kori Ji: Binne Janar Ahmad, ambaliya a makwantai
Hotunan binne Janar Hussain Ahmad da yadda ambaliya ta lalata Makabartar Fataskum da sauran su
A wannan makon mai karewa ’yan bindiga suka kashe wani babban jami’in soji sannan suka yi awon gaba da maidakinsa.
A makon ne kuma ambaliyar ruwa ta share kaburbura a Babbar Makabartar Gashua a Jihar Yobe.
Ga wadannan, da ma wasu labaran da muka kawo muku, a cikin hotuna.
Lokacin da ake shirin binne Manjo Janar Hassan Ahmad, wani babban jami’i a Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya. ‘Yan bindiga ne dai suka kashe Janar din sannan suka yi awon gaba da maidakinsa a Abuja ranar Alhamis (Hoto: Ikechukwu Ibe)
Kaburbura fiye da 650 ne ambaliyar ruwa ta share a Babbar Makabartar Gashua ta Karamar Hukumar Bade, a Jihar Yobe (Hoto: Ibrahim Baba Sale)
Bello Shehu Alkanci daga Jihar Zamfara, wanda ya yi na daya a cikin mutum 30 a babbar gasa yayin Gasar Rubutun Wakokin Hausa a, Jami’ar Usumanu Danfodio da ke Sakkwato daga ranar 12 zuwa 13 ga watan Yulin 2021 (Hoto: Bashir Yahuza Malumfashi)
Wani da ake zargin mai fasa shago ne yana jan wasu kayayyaki a kusa da wani rukunin shaguna da aka barnata a unguwar Vosloorus da ke wajen garin Johannesburg na Afirka ta Kudu ranar 14 ga watan Yuli. Kwana biyar a jere masu fasa shago suka kwashe suna barna duk da sojojin da aka girke don su kwantar da hatsaniyar da ta yi sanadin mutuwar mutum 72 (Hoto: MARCO LONGARI / AFP)
Daya daga cikin baburan da wani matashi dan Katsina ya kera, wanda Gwamna Aminu Masari ya saya a kan kudi N170,000 (Hoto: Kabir Ahmed S/Kuka)
Raguna a kasuwar Layin Bagobiri da ke birnin Kalaba na Jihar Kuros Riba (Hoto: Musa Kutama)