Gani Ya Kori Ji: Muhimman abubuwan da suka faru a wannan makon

Gani Ya Kori Ji na Aminiya ya tattaro muku hotunan wasu abubuwan da suka faru a wannan mako da muke bankwana da shi domin kayatar da ku. Yadda aka yi bikin yaye mahaddata Alkur’ani su 31 a makarantar kungiyar Izala (JIBWIS) da ke Abuja ranar Asabar. HOTUNA: Adam Umar Yadda aka yi bikin yaye mahaddata […]

Gani Ya Kori Ji: Muhimman abubuwan da suka faru a wannan makon

Yadda kasuwar Balogun Alanamu ta Jihar Kwara ta yi gobara. Hoto: Ofishin Gwamnan Jihar Kwara

Gani Ya Kori Ji na Aminiya ya tattaro muku hotunan wasu abubuwan da suka faru a wannan mako da muke bankwana da shi domin kayatar da ku.

Yadda aka yi bikin yaye mahaddata Alkur’ani su 31 a makarantar kungiyar Izala (JIBWIS) da ke Abuja ranar Asabar.
HOTUNA: Adam Umar
Yadda aka yi bikin yaye mahaddata Alkur’ani su 31 a makarantar kungiyar Izala (JIBWIS) da ke Abuja ranar Asabar.
HOTUNA: Adam Umar

 

Iyayen marigayiya Hanifa ke nan, yarinyar malaminsu ya kashe bayan yin garkuwa da ita a Kano yayin da manema labarai ke jin ta bakinsu a harabar Babbar Kotu a Kano da ta yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Luka Kauna da Hannatu Musa ke nan wasu daga cikin matan Chibok da sojoji suka yi nasarar kwatowa bayan sun riga da sun haifi yaransu.
Yadda aka cire tsohuwar rigar Ka’aba da ake kira Kiswaah domin sauya sabuwa a ranar Juma’a wanda ta yi dai-dai da ranar karshe ta shekarar musulunci ta 1443 bayan Hijira. Hoto: Haramain Sharifain
Hanyar Salka zuwa Auna daidai Mararrabar Koso da ke Karamar Hukumar Magama ta Jihar Neja. A halin yanzu an dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a hanyar saboda yadda ambaliyar ruwa ta yi barna. Hoto: Comrade-Zakari Y. Adamu Kontagora.
Dandazon mutane ke nan a Ofishin Hukumar INEC na Jihar Kano yayin da suke jiran mallakar katin zabe ana gab da karewar wa’adin yin katin. Hoto: Salim Ibrahim Umar
Hoton yadda kasuwar Balogun Alanamu ta Jihar Kwara ta yi gobara. Hoto: Ofishin Gwamnan Jihar Kwara

 Yadda mambobin Kungiyar Kwadago da na ASUU suka gudanar da zanga-zangar lumana ta kwana biyu domin mara wa ASUU baya kan yajin aikinta da ya ki ci ya ki cinyewa.