Ganin Ido Bai Hana Cin Kai
Idan ana batun rashawa da cin hanci a duniya, ai kasa ta Najeriya tana gaba. Babu yadda za a yi ka ji ana tabo batun gwanaye da fitattun mutanen da suka gwanance wajen kuruciyar bera ne, a ko’ina a fadin duniyar nan, ba a ambaci wasu shugabannin Najeriya ba. ‘Yan Najeriya sun yi kaurin suna […]
Idan ana batun rashawa da cin hanci a duniya, ai kasa ta Najeriya tana gaba. Babu yadda za a yi ka ji ana tabo batun gwanaye da fitattun mutanen da suka gwanance wajen kuruciyar bera ne, a ko’ina a fadin duniyar nan, ba a ambaci wasu shugabannin Najeriya ba. ‘Yan Najeriya sun yi kaurin suna a duk inda suka dosa, har ma idan an gano su, za ka ga ana ta kaffa-kaffa da su, ko kuma a dinga shisshige musu don an tabbatar sun zo da dimbin dukiyar da za su kashe a banza, wacce kowa ke hakikancewa ba su san zafinta ba. Idan da mutum zai shiga mota tare da dan rakiya, ya zagaye manyan biranen duniya, kamar su New York ko Landan da Belgium da Paris ko Brussels da Berlin, za a dinga nunnuna masa kaddarori da gine-gine da kayayyakin gagari, irin na kece-raini, a ce da shi duk mallakar ‘yan Najeriya ne. A takaice dai a idanuwan al’ummomin duniya, dan Najeriya hamshakin mutum ne, wanda bai san fatara ba, bai kuma damu da ita ba, ganin yadda yake facaka da dukiyarsa a banza.
Baicin dimbin arziki da wadatar da dan Najeriya ke da shi a wasu kasashe, wasu ‘yan wadancan kasashe na girmama shi don abin da za su dan yayyaga daga gare shi, wasu kuma na yi masa kallon wani kasurgumin macuci, wanda bai taimaka wa kasarsa da waccan dukiyar da yake kwance akai; haka nan ‘yan uwa da danginsa da sauran jama’ar kasarsa ke sharbar bakar wahala, suna kwana, suna tashi cikin yunwa da ragga, ba su da aikin yi, balle kudaden sayen magunguna ko biya wa ‘ya’yansu kudaden makaranta. Irin su ne ke kakkafa masana’ntu a kasashen ketare, ‘ya’yan wasu na amfana, suna kuma inganta bankunan Turawa da kudaden da suka sata a kasarsu, kuma ko da sun mutu ba za a komo wa magadansu da ita ba, haka nan za ta salwanta.
An dade da sanin cewa akwai dimbin arzikin Najeriya birjik a kasashen Turai da Amurka, wadanda ‘yan Najeriya suka sace, suka tsibe a can, kuma ko an gano haka, aka kokarta don karbowa ba a samun ingantacciyar nasara game da haka. Sai a dauki dogon lokaci, ana barin kudin sata daga kasar nan, suna haihuwa a bankunan Turawa, kafin a dan tsakuro kadan daga ciki, a maido. Kuma ko da aka taba yin haka ma, kudaden da aka ce wani shugaba guda daya ne ya kwasa daga kasar kadai aka nemi a maido, na sauran kuma ko oho. Watakila sai bayan wafatinsu ne za a san ko nawa ne su ma suka sassace, a tsakuro wani abu daga ciki, a maido mana da su. Mutuwar wadanda suka sace, suka ajiye su a ketare za ta kara haramta wa kowa wadancan kudaden a Najeriya.
To, yanzu ga wata badakala can an bankado a kasar Panama da ke makwabtaka da kasar Amurka, inda aka ce an gano boyon wasu azzaluman shugabanni da jami’an gwamnatocin wasu kasashe, ciki har da Najeriya, a wasu bankunan musamman na halasta dukiyar haram, don a ji dadin sarrafa su a wasu kamfanonin da za a iya maida su kasashen da aka sassace su. Wannan tonon sililin da ake yi ya zame abin kunya ga wasu da suka nemi yi wa kawunansu kiyamul-laili, domin kuwa har FirayimMinistan kasar Iceland, Sigmundur Gunnlaugsson ya sauka daga mukaminsa, duk kuwa da hasashen da ake yi na cewa bai karya wata doka ba game da haka. Matarsa ce, Sigurlaug Palsdottir, ba shi ba, ake zargi ta bude ajiya da dukiyar haram a bankunan kasar Panama, kuma a karkashin dokar kasar Iceland ba lallai ba ne sai ya bayyana wa dumiya abin da matarsa ke ciki da kuma abubuwan da ta mallaka. Amma a sakamakon hayaniya da hayagagar jama’a kasar wacce dokokinta ba masu tankwaruwa ne ba, sai kawai FirayinMinstan ya sauka daga mukaminsa, ya kuma ajiye kwallon mangwaro don ya huta da kuda. Haka nan ma a kasar Birtaniyya, FirayinMinista Dabid Cameron ma na fuskantar kalubale dangane da haka, kuma duka da cewa dukiyarsa da aka gano a bankunan Panama ya ce ta gadon da tsohonsa ya bar masa ce, jama’a suna nan suna ta matsawa sai ya kara gaba.
To, ta ina sunayen ‘yan Najeriya suka firfito a wannan harkallar? An ambaci sunan Shugaban Majalisar Dattijai, wanda ya yi kememe, ya ce bai san wancan batun ba, amma kuma daga bisani sai ya kara, ya ce kudin da ake cewa nasa ne, mallakar matarsa ne, Toyin wacce ta samu sakamakon wani gidan iyayenta da ta sayar a Lagos. Amma lauyoyin matar tasa sun ce ba haka batun yake ba, ita ba ta sayar da wani gidan iyayenta ba a Lagos, dukiyar dai ta Saraki ce, ta kashin kansa, shi kadai, ba gauraye. An kuma fitar da wata takardar da ta nuna rubutun hannun Saraki da kansa da kuma sa hanunsa bisa yarjejeniyar sayen daya daga cikin kamfanoninsa daga wajen matarsa akan kudi Fam miliyan uku, sa’ilin da yake bisa kujerar Gwamnan Jihar Kwara.
To, bayan Sanata Bukola Saraki kuma sai tsohon shugaban Majalisar Dattijai, Cif Dabid Mark, wanda bayan an yi mar tonon silili sai ya ce ya yi nazarin bayanan da aka bayar, amma bai ga inda aka ambaci sunansa ba. To amma sai dai kungiyar da ke tonon silin ta ce babu yadda za a yi Dabid Mark ya ya karyata wancan batun, alhali kuwa sauran jama’ar da aka ambaci sunayensu sun amince da zargin da aka yi musu. An kuma ambato sunan Janar Theophilus Danjuma a cikin waccan rikita-rikitar ajiyar kudaden Haram a Panama, kuma shi ne dan Najeriya, daga cikin wadanda aka yi wa tonon silili, da ya ki cewa uffan game da haka. dayan kuma da aka ambata shi ne James Ibori, tsohon Gwamnan Jihar Delta, shi yana tsare ne kurkukun kasar Birtaniyya, saboda haka nan ba a ji ta bakinsa ba.
Kodayake an ce zargi ba abin kamawa ba ne sai an tabbatar da shi a matsyin hakkun, ya kamata a duba, don a tabbatar da gaskiyar haka, kada ganin ido ya hana cin kai. Wanda duk aka ambaci sunansa sai ya fito ya kare kansa, a gaban Hukumar EFCC, wacce za ta hanzarta kammala bincike don ita ma ta gaggauta gurfanar da marasa gaskiya game da haka gaban kotuna don yin hukunci. Dukiyar ‘yan Najeriya ce ake zargin an sace, an tsibe a wata kasa, to bai dace ba a ce za a kau da kai, a kyale wasu can su yi ta tumurmusar ta ba a banza, alhali kuwa ana fama da karancin masana’antun da za a iya kakkafawa da wadancan kudaden domin ‘yan Najeriyan da ke fama da rashin aikin yi su murmure, har su tayar da komada. An dai ce ranar wanka ba a boyon cibi, wanda kuma ya debo da zafi bakinsa.