Gara duk ’yan takarar PDP su fadi dankwambo ya sake zama Gwamna – Usman Kumo

dan Majalisar Tarayya daga Mazabar Akko a Jihar Gombe Alhaji Usman Bello Kumo ya ce gara duk ’yan takarar PDP su fadi a zabe mai zuwa kuma bai damu ya fadi a zabe ba idan Gwamna dankwambo zai sake cin zabe karo na biyu. dan Majalisar ya bayyana haka ne ga shugabanin Jam’iyyar PDP n […]

Gara duk ’yan takarar PDP su fadi dankwambo ya sake zama Gwamna – Usman Kumo
Gara duk ’yan takarar PDP su fadi dankwambo ya sake zama Gwamna – Usman Kumo

dan Majalisar Tarayya daga Mazabar Akko a Jihar Gombe Alhaji Usman Bello Kumo ya ce gara duk ’yan takarar PDP su fadi a zabe mai zuwa kuma bai damu ya fadi a zabe ba idan Gwamna dankwambo zai sake cin zabe karo na biyu.

dan Majalisar ya bayyana haka ne ga shugabanin Jam’iyyar PDP n jihar a ranar Litinin lokacin da ya mayar da fom din da ya cike don tsayawa takarar Sanata a Gombe ta Tsakiya.
Ya ce yana neman kujerar ce saboda Sanatan da ke kan kujerar ya canja sheka zuwa Jam’iyyar APC duk da shugaban Majalisar Dattawan Sanata Dabid Mark bai amince da canjin shekar
tasa ba.
Usman Bello Kumo, ya ce don mene ne al’ummar Jihar Gombe suke da ja kan sake zaben Gwamna Ibrahim dankwambo, a karo na biyu wanda in aiki ne ya yi kowa ya gani?
Ya ce zagi da kushe ko cin mutunci da ake yi wa ’ya’yan Jam’iyyar PDP a jihar na cewa ana aiki ba a ba da kudi bai kamata ya sa gwiwarsu ta yi sanyi ba, su fito don ganin an dawo da dankwambo karagar mulki a shekarar 2015.
“In dai wakilcin mutane shi ne a yi aiki a dasa mutunci da adalci a zukatan mutane to na sadaukar da wannan fom da takarar da nake yi don cin zaben Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo,” inji Kumo
Ya kara da cewa, “Na yarda na fadi in dai dankwambo zai ci zabe kuma in duk Jihar Gombe
kowanne dan takara zai fadi a zabe amma a samu dankwambo ya ci zabe gara haka saboda alherin da yake yi wa al’ummar jihar.”
Usman Kumo, ya gode wa abokan takararsa da suka janye suka bar masa takarar ba don ya fi su ba, sai don saboda suna ganin shi ya fi dacewa a daidai wannan lokaci. Kuma ya gode wa al’ummar yankinsa na Gombe ta Tsakiya bisa hadin kai da goyon baya da suke ba shi a siyasance.