Gara mutum ya zama arne da ya zama munafuki – Fafaroma
Fafaroma Francis ya sake caccakar waxansu mabiya cocinsa na Katolika, inda ya nuna ya fi kyau mutum ya kasance arne ko mushiriki fiye da waxansu daga cikin ’yan Katolika da “dama” da ya ce suna bin cocin da munafunci.Wannan kalami ya fito ne a lokacin da yake huxubar safiya a gidansa a ranar Alhamis xin […]
Fafaroma Francis ya sake caccakar waxansu mabiya cocinsa na Katolika, inda ya nuna ya fi kyau mutum ya kasance arne ko mushiriki fiye da waxansu daga cikin ’yan Katolika da “dama” da ya ce suna bin cocin da munafunci.
Wannan kalami ya fito ne a lokacin da yake huxubar safiya a gidansa a ranar Alhamis xin makon jiya, inda ya ce: “Varna ce ka faxi wani abu, amma ka aikata akasinsa. Wannan munafunci ne.”
“Akwai masu cewa “Mu ’yan Katolika ne, koyaushe ina zuwa addu’a, ina cikin wannan ko waccan qungiya,” inji jagoran mabiya Katolika biliyan xaya da miliyan 200, kamar yadda gidan Rediyon Vatican ya wallafa kuma kafar labarai ta Reuters ta ruwaito.
Tun zavensa a shekarar 2013, Fafaroma Francis ya sha gaya wa mabiya cocin Katolika, ciki hard a limamai da sauran mabiya su riqa aikata abubuwan da addinisu yake koyarwa.
Kuma a cikin huxubobinsa Fafaroma Francis ya sha la’antar cin zarafin yara qanana ta hanyar lalata das u,tare da bayyana hakan da cikakken “aikin Shaixan,’ ya shaida wa manyan limamansa cewa su guji yin wasu abubuwa da za su riqa nuna tamkar su “’Ya’yan Sarakuna ne.”
Kuma qasa da wata biyu da zavensa Fafaroman ya ce, ya kamata Kiristoci su riqa xaukar arna da mushirikai a matsayin mutanen kirki kamarsu.