Gara rayuwar Najeriya da ta Saudiyya -Yakubu Usman
Aminiya ta samu tattanawa da wani dan Najeriya mai suna Yakubu Usman, mazaunin kasar Saudiyya da yawo gida Najeriya saboda bakar wahalar rayuwa da ya sha. Yakubu Usman, wanda ya yi aiki a kamfanin gine-gine na Bin Laden a matsayin lebura, ya ce mutane sun jahilci yadda rayuwa take a kasar Saudiyya, shi ya sa […]

Aminiya ta samu tattanawa da wani dan Najeriya mai suna Yakubu Usman, mazaunin kasar Saudiyya da yawo gida Najeriya saboda bakar wahalar rayuwa da ya sha. Yakubu Usman, wanda ya yi aiki a kamfanin gine-gine na Bin Laden a matsayin lebura, ya ce mutane sun jahilci yadda rayuwa take a kasar Saudiyya, shi ya sa suke sha’awar zuwa can neman kudi. Malam Yakubu ya ce rayuwa a Najeriya ta fi sauki. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?
Sunana Yakubu Usman, yau shekarata 44 a duniya. Ni dan asalin garin Azare ne a Jihar Bauchi kuma na yi kusan shekara 20 a Jihar Legas. Ina da mata biyu da ’ya’ya bakwai. Na taba aikin soja, inda na yi ritaya saboda rashin lafiya bayan na yi shekaru biyar a ciki. Na yi aikin tukin tirela a garin Jega, inda na yi shekara uku. Na koma sana’ar sayar da lemu da ayaba da kwakwa a garin Jos. Na bari na dawo Legas na kama kasuwancin sayar da doya, daga bisani sai na koma sayar da kayayyakin wuta. Daga bisani sai na bari na koma yin acaba.
Aminiya: Wane dalili ne ya kai ka kasar Saudiyya?
Ni dai Allah ne Ya sa zan je. Na yi wani mafarki cewa ina dauke da itace, sai na ga wadansu bayin Allah suna zagaya wata bishiyar tsamiya suna hailala, ni kuma sai na tsaya da kayan itacena, sai daya daga cikinsu ya ce, ‘Kai kuwa bawan Allah daga ina kake?’ Sai na ce daga gona nake, sai ya ce, ‘Kana so ka zo nan inda muke?’, sai na ce ina so na zo mana, sai ya ce, ‘In Allah Ya yarda za ka zo.’ Bayan kwanaki da yin mafarkin sai kawai na ji wata yayata ta kira ni daga Saudiyya ta ce ta biya mini kudin zuwa can, sai na ce mata ni ba za ni ba, gara ta turo mini da kudin na sayi mota, sai ta ce ta riga ta biya babu yadda za a yi, dole sai dai na tafi na je na nemi kudi. Sai na fara shirye-shiryen tafiya har lokaci ya yi, muka tashi a jirgi muka tafi, kamar mafarki. Da na je sai da na yi wata biyu ban samu ko riyal daya ba, ba na aikin komai sai zaman banza.
Aminiya:Ta yaya aka yi ka samu aiki?
Akwai wani bawan Allah mutumin Jihar Sakkwato da muke shan shayi a kofar gidansa, mai suna Jamil, sai ya tambaye ni cewa, shin wai ba na aiki ne? Sai na ce masa ba na aiki. Sai ya ce mu je harami akwai aiki da zai samar mini. Sai muka je aka dauke ni aiki a kamfanin gine-gine na Bin Laden a matsayin lebura a sashen gini. Shi wannan mutum yana da ’ya’ya. daya yana aikin soja daya kuma yana aikin askar. Aka ba ni inifom. Sai na fara aiki gadan-gadan.
Aminiya: A lokacin da kake zaune a kasar Saudiyya me ya fi ba ka mamaki?
Kafin na je ina jin labarin cewa a Saudiyya ba a zaman banza, ana samun aikin yi kuma ba a wasa da addini, sai da na je sai na ga ba haka ba ne. Ba a samun aiki cikin sauki kuma na ga wadanda ba sa sallah kuma ba sa azumi. Da na rika yin mamaki, sai aka ce mini ai irin mutanen da ba sa sallah ba sa azumi suna da yawa a Saudiyya. Sai ga shi matanmu da aurensu, amma da sun je sai su kara yin aure. Akwai kuma wadanda suna zaune da mazajensu a can sai su tafi wata unguwa su sake yin aure. Idan tana gidanka matarka ce, kuma idan ta tafi gidan wancan mijin da ta aura, to mijinta ne. Haka suke rayuwa da maza biyu a lokaci guda. Wata har aure uku take yi saboda tsabar son abin duniya. Idan ka tafi da matarka Saudiyya, idan ka yi sake sai ta fi karfinka, saboda hure mata kunne da wadansu matan za su yi. Ni idan mace aka ce ta dawo daga Saudiyya ko zinari zan rika kankara a jikinta, wallahi ba zan aure ta ba, saboda na zauna a can na ga irin dabi’un da mutane suke yi. Wani abin da ya ba ni mamaki shi ne, za ka ga matanmu sun shiga shagon sayar da kaya, sai daya ta tsaya mai shagon yana matsa mata nono, sauran kuma suna yi masa satar kaya. Wallahi-wallahi, idan da ni shugaban kasa ne duk dan Najeriyar da ya je Saudiyya ba zai zauna neman kudi ba, dole sai ya dawo gida.
Aminiya: Me ya sa ka dawo Najeriya?
Abin da ya sa na dawo, na tafi ne na bar baya da kura. Ina da mata biyu a nan Najeriya da ’ya’ya. Sannan kuma gaskiya na sha wahala sosai a kasar Saudiyya. Saboda aikin karfi na yi. Akwai lokacin da na dauki buhun siminiti 50 a rana daya ina kaiwa bene mai hawa da yawa. Kuma gaskiya zaman Saudiyya yana da mutukar wahala idan ka kwakwatanta da namu na Najeriya. Zaman Saudiyya idan ba ka kai zuciyarka nesa ba, ba za ka iya ba. Na rantse da Allah ban taba daukar buhun siminti a kaina ba sai a kasar Saudiyya. Akwai lokacin da Balaraben ya kara mini kudi saboda irin aikin da na yi. Gaskiya gara dan Najeriya ya zauna ya nemi arziki a kasarsa, ya fi sauki.
Aminiya: Ina batun mata masu barace-barace da masu bin bola da kuma masu sayar da muggan kwayoyi?
Wadannan su ne suke bata wa kasarmu suna. Za ka ga mace tana bara tana zubar da mutuncinta, idan dare ya yi sai su rika shiga lunguna ana yin amfani da su. Tun ina jin labari har na gani da idona. Haka ma za ka ga wata tana bin bola har ta haukace. Akwai wata tsohuwa da mota ta kade ta da aka duba kugunta sai aka ga kudi fiye da miliyan uku a tare da ita. Su kuwa masu sayar da muggan kwayoyi su ma haka suke ta fama. Wadansu a kama su, wadansu kuma ka ga babu abin da suka tsinana, sai harkar shaye-shaye.
Aminiya: Wace shawara za ka bai wa masu sha’awar tafiya Saudiyya neman kudi?
Ga duk mai hankali, ya kamata ya sauya ra’ayi. Ka san mutane ganin kitse suke yi wa rogo. Wani idan ka fada masa gaskiya, sai ya ga bakin ciki kake yi masa. Akwai wani abokina da na ba shi shawarar kada ya je, sai ya ki ji, ya sayar da gidansa da motarsa ya tafi. Mako biyu kawai ya yi a Saudiyya ya dawo Najeriya saboda wahalar da ya sha. Ya dawo yanzu ba gidan ba motar.