Gararumar garka da gayauna

Babu abin da ke firgita Haurobiyawa illa lashe-lashen uwar jiki da cutar kusu yi wa al’umma. Hasalima mutum zai iya has ashen cewa, saman-dagari da tarko na cin kasuwar su a kasar nan. Abin tambaya a nan shin kusu ne musababbin lashe uwar jiki har ta kai bingirewa, ko kuwa akwai akasin haka a binciken […]

Gararumar garka da gayauna
Gararumar garka da gayauna

Babu abin da ke firgita Haurobiyawa illa lashe-lashen uwar jiki da cutar kusu yi wa al’umma. Hasalima mutum zai iya has ashen cewa, saman-dagari da tarko na cin kasuwar su a kasar nan. Abin tambaya a nan shin kusu ne musababbin lashe uwar jiki har ta kai bingirewa, ko kuwa akwai akasin haka a binciken masana kimiyyar inganta garkuwar jiki?
Kowa yasan wannan makaranta ba ta tare da kusu da ’yan matan jaba da gafiya, amma kiyayyar mu ga wadannan miyagu ba za ta sanya mu ki yi musu adalci ba. Domin rashin adala ke haifar da juhala. Wannan ne dalilin da ya sa nike son tabbatar da batun Malam mai yaren Hau-hau wajen hawansa ba tare da sa-in-sa ba, inda ya furta cewa, “idan kusu na da sata, daddawa ma na da wari.’ Haurobiyawa mu muke tara curin tsummokarai da nau’ukan kazanta iri-iri, shi yasa kusu ke zirya a tsakanin akurkin al’umma da rumfunan kasuwanni, har ma da farfajiyar Bokan Turai. Idan kuwa batuna ya zama dutse, ina ganin akwai bukatar mu sake salon inganta muhalli, musamman garka da gayauna, tunda a can muke dasa kayan dundume kururu.
Kafin in ci gaba da bayanin garka da gayaunar shuke-shuke da dashen tsirrai da furannin kallo, ya kamata mu fasko cewa, miyagu sun mayar da lalitar kasa garka da gayaunar kwasar gararuma, al’amarin day a haifar musu da asakala tsakanin su da Iro mugun madambaci, mai hana magu-magu. Kuma muna da tabbacin cewa, a wannan karon za a yi gwagwarmaya da arangama da masu fashi da mukami ko da dabara, sabanin yadda aka aiwatar a zamanin rubdigau da Loma-a-murde. Domin ni na yanke cewa, Mace-mai Fari-da-idanu a cikin bakar kwalba ta fi su yin artabu da kusu da ’yan matan jaba da gafiya, wadanda suka lashe uwar jikin kasa, suka jigata burgamen adana dukiyar kasa.
Sanin kowa ne a garka da gayauna ake ribato mangoro da gwaba da lemu da ayaba da jimbirin wake da sauran nau’ukan gararumar kayan marmarin more rayuwa. Irin nau’ukan lagwadar da ake lunkumewa a bakuna daga kayan marmari na ingata uwar jiki, musamman a wajen aikin markade da nika kayan dundume kururu, amma duk da haka idan suka gwamu da kwayoyin cututtuka wadanda na mujiya ba ya iya fasko su; kodayake masana na iya ramfo su, ta hanyar amfani da tabaron Bokan Turai.`
Batu na ingarman karfen karafan kwangiri, a ranar Tabawa ranar samu, a watan Janye-wuri, jaridar Dalilin-taron su, a shafi na sili da karamin lauje ta bijiro da batun kassara liyafar lafiya da wakilin rafkiya daga Jihar Gumbar-bebe, a karkashin tutar jam’iyyar mai maganin zogi da radadin kurungu ya bijiro da shi, inda aka ce mutum malala karamin lauje ke shekawa barzahu a sanadiyyar gubar da ke damfare a kayan dunbdume kururu. Wakilin rafkiyar ya gabatar da kudurin sa, wajen neman samar da dabarun zamani na sarrafa kayan da aka samar daga sana’ar na-duke da limbu-limbu cikin lambu. Idan muka yi faskaren ma’anoni da kyau za mu fasko cewa, wannan wakili ya yunkuro don rafke cututtukan da ke damfare a gararumar garka da gayauna.
’Yan makaranta da gungun masu koyon watsattsake da buda wagsagen littattafai a farfcajiyar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, akwai bukatar mu bunkasa kimiyyar kimtsa miya, ta tafi daidai da kimiyyar binciken masana, ta yadda da zarar garka da gayauna sun inganta za mu shirya liyafa, mu lafe a gefe, mu karya kashin kazar da aka kyafe, amma ban da bankar lofe.
Batun gandun daji kuwa, tuni muka kamala shi, inda muka bijiro da batutuwan da suka shafi katafaren koren shinge. Da zarar hukumomi sun sauke nauyaye-nauyayen da ke kan kurungun su, ina ganin ko da kusu ya yi sata, ya damalmala mana kayan dundume kururun da muka ribato daga garka da gayauna, tabbas ba zai yada cututtukan da za su caccaki uwar jikin al’umma ba.
Wani al’amari mai faranta zukata, shi ne Usainin-Babajo, mataimakin shugaban kasar Haurobiya, ya koka kan yadda gama-garin Haurobiyawa masu fama talalar talauci ke ganin tasku wajen kula da matsalolin uwar jiki. Sai kuma ya bayyana yadda a ka ware wani kaso a cikin kundin baje kolin Hauro na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama don shawo kan fatara da ke fatattakar al’umma. Kai wasu kafafen kwakwazon ma baza wa duniya suka yi , wai Usainin-Babajo ya yi alwashin tube fatarin fatara da ke kakabe a jikkunan mutum malala sili da zagaye da zagaye.
Gararumar gayauna da garkar al’umma duk miyagun jam’iyya mai dan boto da sanda jirge sun jide ta. Mu kuwa sun bar mu muna ta haure-haure da hauragiya. Sai dai su ma suna dandana kudar su.
Yau kowa ya ga Samun bom da sauki a koma; ga Mayen-tutu da Baffan-rawa na cikin gungun manyan kusu da ’yan matan jaba da gafiya babban lauje da babban lauje da ke kada wa Haurobiyawa jauje a kudar su. Mu kuma sun bar mu a cikin dama-dama da kurda-kurdar wasan Samson-siya-siya, inda suka karke da yi mana damo-da-kura-da-diyya.
Haurobiyawa, mu hada karfi da karfen kwangiri a bargar ingarman sukuwar kasar mu, wajen ganin an yi maganin cututtukan da kusu ke yadawa, musamman wadanda suka lashe lumanar uwar jikin tsimi da tanadin dukiyar kasa. Tsarin tsimi da ta’adinku ya kasssara kasa, har ta fara kasa-kasa, sai shbugabanni suka fara cafko ku. ’Yan matan jaba da gafiya kuma ba zan kyale ku ba, har sai Baban-burin-huriyya ya cafko ku, domin kwashi kwaraf din da kuka yi shi ya tsunduma al’umma cikin halin kaka-ni-ka-yi!