Garbai ne ya lashe zaben cike gurbin dan majalisar dattawan Barno ta tsakiya
Hukumar Zabe mai zaman kanta ta INEC ta jihar Borno ta bayyana Kaka Bashir Garbai ne ya lashe zaben cike gurbin dan Majalisar Dattawan jihar mai wakiltar Barno ta tsakiya wanda aka gudanar a karshen makon da ya gabata. Da yake ayyanna samun nasarar a lokacin da aka kammala tattara alkaluman zaben, Baturen Zaben, Farfesa […]
Hukumar Zabe mai zaman kanta ta INEC ta jihar Borno ta bayyana Kaka Bashir Garbai ne ya lashe zaben cike gurbin dan Majalisar Dattawan jihar mai wakiltar Barno ta tsakiya wanda aka gudanar a karshen makon da ya gabata.
Da yake ayyanna samun nasarar a lokacin da aka kammala tattara alkaluman zaben, Baturen Zaben, Farfesa Muhahammad Fannami, ya ce Jam’iyyar APC ne ta samu nasara da kuri’u Dubu 120 da 639, sai kuma jam’iyyar PDP da ta biyo bayanta da kuri’u Dubu 32, 346, ya ce a don haka Kaka Bashir Garbai shi ne ya lashe wannan zabe saboda ya cika dukkan sharuddan da doka ta tanadar a don haka shi ne zababbe a jerin ’yan takarar4.’’
Zababben dan takarar dan Majalisar Dattawan, Kaka Bashir Garbai, ya yi alkawarin yin aiki tukuru, ta yadda zai ciyar da yankinsa gaba,’’Zan yi kokarin ganin cewar an samarwa da matasa aikin yi don dogaro da kansu, ta yadda za a rage zaman kashe wando, zan kuma yi kokarin ganin an gyara garuruwan ’yan gudun hijira don su koma su samu natsuwa kamar kowa, kana zan kokarta wajen ciyar da jihar mu gaba.’’
Ita kuwa Jam’iyyar PDP, wadda dan takararta ya sha kaye, ta ce ba ta amince da wannan sakamakon zaben ba, Kaka Bolori shi ne dan takarar jam’iyyar PDP, ya ce zai garzaya Kotu, “Ni ban amince da wannan sakamakon zaben ba, domin kuwa an tafka mummunan magudi tare da hadin bakin hukumar zabe, domin kuwa muna da hujjoji da shaidu kwarara, wadanda suka nuna cewar an tafka magudi musamman a Sansanonin ‘yan gudun hijira, kuma jami’an tsaro sun yi wa magoya bayanmu duka, sannan kuma mun kama inda wasu daga cikin jami’an tsaro suke jefa kuri’a, saboda haka ba za mu amince da wannan sakamakon zabe ba, a don haka za mu garzaya kotu.’’
To amma Shugaban tawagar masu sa ido a zaben, wanda Hukumar Zabe ta amince masu su sanya ido akan zaben, Mista Gebrail Nwambu, ya tabbatarwa da manema labarai cewar wannan zabe sahihi ne,’’An gudanar da wannan zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma Hukumar Zabe ta yi adalci da gaskiya a zaben, saboda haka dukkanmu tawagar masu sa’ido mun tabbatar kuma mun shaida wannan zabe sahihi ne kuma karbabbe, ingantacce.’’
Barno ta tsakiyar dai ta kunshi kananan hukumomi takwas ne, wadanda suka hada da Dikwa da Mafa da Konduga da Bama da Kala-Balge da Jere da Gamboru Ngala, da kuma Majalisar Mulki ta birnin Maiduguri, an kuma gudanar da zabenne a garin Maiduguri saboda akasarin ‘yan gudun hijiran da suka fito daga wadannan wuraren suna gudun hijirar su ne a Sansanonin gudun hijira a garin Maidugurin, wannan zabe cike gurbi dai an yi shi ne a sakakamakon rasuwar dan Majalisar Dattawan mai wakiltar wannan yanki na Barno ta tsakiya, marigayi Sanata Ahmed Zanna Khalifa, wanda Allah ya karbi ransa a watannin baya.