Garejin da mata zalla ke aikin gyaran mota

Babu namiji ko daya a tawagar matan da ke aiki a sansanin kanikawa na garin Zuba Abuja

Garejin da mata zalla ke aikin gyaran mota

Madam Favour tare da ‘yan matan da ke koyon aikin kanikanci a garejinta

Sansanin kanikawa na garin Zuba a Abuja, waje ne da ya yi fice a wajen gyaran motoci kamar na Apo da ke mabambantan kusurwowi a yankin Birnin Tarayya.

Aminiya ta ziyarci wajen a ranar Talatar da ta gabata inda ta yi kicibis da wata mace mai kamar maza da ke aikin gyaran mota tare da wasu ’yan mata da ke karkashinta a matsayin ’yan koyo.

Madam Favour Okonkwo wadda ’yar asalin garin Awka ne da ke Jihar Anambra, ta ce sha’awarta ta yin sana’ar ya samo asali ne tun lokacin da take karatu a makarantar sakandaren koyon aikin kere-kere a yankin nasu.

Ta ce daga bisani ta auri mijinta mai suna Mista Valentine Okonkwo wanda bakanike ne, yana kara mata kwarin guiwa, sannan suke aiki a sansani daya yanzu.

Madam Favour tana tattaunawa kan wani inji da ke gabansu

Ta ce a bangarenta tana aikin ne tare da ’yan mata hudu da ke karkashinta a matsayin masu koyo, shi kuma mijin nata akwai samari biyar a karkashinsa.

‘Na rike kanikanci da hannu biyu’

Ta ce Allah Ya azurta auren nasu da ’ya’ya shida ya zuwa yanzu.

Uwargida Favour ta ce baya ga karatun sakandare da ta yi, ta halarci kwasa-kwasai da tarukan kara wa juna sani a harkar, inda ta fadada saninta a aikin na kanikanci.

“Mun fara sana’ar a garin Anaca a jiharmu ta Anambra, sannan daga baya muka dawo nan Abuja a shekara ta 2010.

“Nakan halarci gareji ko da ina dauke da juna biyu duk da cewa ba abu ne mai sauki ba.

“Zan yi abin da na iya wanda ban iya ba sai wasu su yi”, inji ta.

Game da yadda take hada sana’ar da kula da gida kuma, uwargida Favour ta ce, “Komai a rayuwa ya danganci yadda ka tsara shi — idan ka tsara rayuwarka da kyau to za ka tafiyar da komai cikin sauki; amma idan ka gaza, to rayuwar ce za ta tsara ka”.

Ta ce duk da haka, ta fuskanci matsaloli da dama har ta kai ga a wasu lokutan ba ta iya zuwa wurin aiki saboda dalilai na bukatun gida.

“Wadanda suka fahimci matsalata kan yi mini uzuri har na gama da bukatun gida sannan na zo na yi musu aiki ba tare sun yi fushi ba”, inji ta.

Ta ce kwai kuma masu yunkurin raunana mata gwiwa. “Wasu mutanen kan fuskance ni su ce mai ya sa na sa kaina a aikin da maza aka sani da shi; wasu kuma su ce mace kyakkyawa kamata bai kamata ta yi aikin ba, da dai sauransu.

“Sai dai hakan bai taba raunana min gwiwa ba, saboda na zaba wa kaina sana’ar a matsayin abin dogaro.

“Ni a wajena burin rayuwa bai wuce biya wa kai bukatu ba, sai kuma na iyali da na dangi.

Uwargida Favour a lokacin da take yi wa Aminiya bayani a garejin nata

Nasarar da na samu a kanikanci —Madam Favour

Bakanikiyar ta ce zuwa yanzu ta yaye mata biyu da ta koya wa sana’ar, sannan akwai hudu a gabanta da ke koyan aikin a yanzu.

Da take tsokaci a kan ’ya’yanta, ta ce ba za ta jira har sai sun nuna suna sha’awar sana’ar ba kafin su shige ta.

Ta ce tuni ta tsunduma su a cikin sana’ar saboda za ta zama mai amfani a garesu a yanzu ko nan gaba.

“Yawancin ’ya’yana mata ne, kuma tare da su muke a nan a lokacin kullen coronavirus da ya shafi makarantu, inda suke aiki tamkar kwararru.

“Sai dai yanzu sun koma makaranta inda wasu daga cikinsu ke halartar makarantun kwana”, injita.

Ta ce ta samu nasarori da dama a rayuwa ta hanyar sana’ar ciki har da kula da kai da kuma iyali.

“Kamar akasarin ’yan Najeriya ni ma ba na rokon abin da zan ci, sai dai na ciyar da wasu kuma ba na shiga damuwa wajen biyan kudi da ake nema daga wajena kamar na karatun ’ya’yana, ko na asibiti da dai sauransu. Sannan nakan bai wa yaran da ke gabana a wajen sana’a kudin kashewa bakin gwargwado kamar na abinci,” inji ta.

Ta ce hakan babbar nasara ce a wajenta kuma mutum kan shafe shekara uku zuwa hudu kafin a yaye shi daga wajen, tare da bude wajen kanikanci na kansa.

Sana’ar kanikanci ne burina

Aminiya ta zanta da daya daga cikin ’yan matan da ke koyon sana’ar a wajenta mai suna Victoria John mai shekara 18, inda ta ce koyon sana’ar kanikanci na daya daga cikin burinta na rayuwa.

Victoria John, daya daga cikin ‘yan matan da ke koyon kanikanci a garejin.

Ta ce karatunta ya tsaya ne a aji ukun karamar sakandare, sai dai tana da shirin komawa makaranta a nan gaba.

Budurwar ta ce duk da cewa ba ta wuce shekara daya ba da fara koyon sana’ar, zuwa yanzu ta koyi bangarori da dama na aikin kuma tana da burin zama kwararriya kamar uwargindan tata.

Sana’a na da amfani ga mata

Mijin matar mai suna Valentine Okonkwo, ya ce garejin nasu ya yi fice ne wajen gyaran motoci kirar Jamus, kamar Marsandi da Audi da BMW da Volswagen da dai sauransu.

Da yake bayani a kan abin da ya karfafa masa gwiwa ya bar matarsa shiga harkar kanikanci tare da bai wa ’yan mata damar zama a karkashinta, Injiniya Valentine ya ce koyar da mace sana’a domin dogaro da kai abu ne mai kyau.

Ya ce hakan zai kuma taimaka mata a al’amuranta da na iyali, sannan ya kawar mata da takaicin rayuwa da ke ba da kafar cin zarafi, inji shi.

“A ganina duk abin da namiji zai yi, akwai macen da za ta iya yi, idan ma ba ta yi fiye da hakan ba”, a cewarsa.

Mista Valentine ya ce burinsa a yanzu shi ne komawa sabon gareji babba da ya kafa a garin Tungan-Maje a Abuja, wanda ya ce zai iya daukar ’yan aiki da yawa fiye da na yanzu.

“Sannan ina da burin mallakar kayan aikin daga motoci iri-iri, da na tantace su da na cire taya ko daidaitawa, don bunkasa sana’armu”, inji shi.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7