Gareth Bale ne ya fi kowane dan kwallo gudu

Wata mujalla da ake wallafa wa a Meziko mai suna Pachura ta yi wani bincike inda ta zakulo ’yan kwallo 10 da suka fi gudu a duniya. Wanda ya kasance na daya shi ne shahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen mai suna Gareth Bale. Mujallar ta ce a binciken da ta yi, ta […]

Gareth Bale ne ya fi kowane dan kwallo gudu
Gareth Bale ne ya fi kowane dan kwallo gudu

Wata mujalla da ake wallafa wa a Meziko mai suna Pachura ta yi wani bincike inda ta zakulo ’yan kwallo 10 da suka fi gudu a duniya.

Wanda ya kasance na daya shi ne shahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen mai suna Gareth Bale. Mujallar ta ce a binciken da ta yi, ta gano Bale yana gudun da ya kai na kilomita 36.9 a cikin awa daya daga nan sai Jurgen Damm da yake kwallo a kungiyar kwallon kafa ta Pachuca da ke Meziko da aka kiyasta yana gudun kilomita 35.23 a awa daya. Sai na ukunsu Antonio balencia dan kwallon Manchester United da ke gudun kilomita 35.1 a awa daya. Sai Aaron Lennon dan kwallon Tottenham na Ingila mai gudun kilomita 33.8 a awa daya sannan sai Cristiiano Ronaldo dan kwallon Real Madrid na Sifen da ke gudun kilomita 33.6 a awa daya.
Sauran sun hada da dan kwallon Arsenal da ke Ingila Theo Walcott wanda aka kiyasta yana gudun kilomita 32.7 a awa daya sai Lionel Messi, dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen da ke gudun kilomita 32.5 a awa daya sai Wayne Rooney na kulob din Manchester United da ke Ingila da ke gudun kilomita 31.2 a awa daya yayin da Frank Ribery dan kwallon Bayern Munich da ke Jamus yake gudun kilomita 30.7 a awa daya sai na 10 a jerinsu watau dan kwallon Real Madrid da ke Sifen Sergio Ramos da ke gudun kilomita 30.6 a awa daya.