Gareth Bale zai shafe mako uku yana jinya

Shahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen Gatreth Bale ya ji raunin da zai sa ya shafe kimanin makonni uku ba tare da ya buga kwallo ba. Rahoton ya ce dan kwallon ya samu rauni ne a jijiyoyin da ke karkashin cinyarsa ta hagu al’amarin da ya sa aka canza shi minti hudu kacal […]

Gareth Bale zai shafe mako uku yana jinya
Gareth Bale zai shafe mako uku yana jinya

Shahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen Gatreth Bale ya ji raunin da zai sa ya shafe kimanin makonni uku ba tare da ya buga kwallo ba.

Rahoton ya ce dan kwallon ya samu rauni ne a jijiyoyin da ke karkashin cinyarsa ta hagu al’amarin da ya sa aka canza shi minti hudu kacal da fara wasa a tsakanin Malaga da na Madrid a ranar Asabar da ta gabata a gasar La-Liga ta Sifen
“A binciken da Likotocin da ke kulob din Madrid suka gudanar a kan Gareth Bale a jijiyoyin da ke cinyarsa ta hagu, an tabbatar dan kwallon ya ji raunin da zai sa ya kwashe makonni uku yana jinya ba tare da buga kwallo ba”, a sanarwar da kulob din ya fitar kuma ya aikawa kafofin watsa labarai.
A tattaunawa da wata jarida a Italiya, Kocin Madrid Carlo Ancelotti ya ce Bale zai shafe makonni ba tare da ya yi kwallo ba, don haka kulob din yake kokarin maye gurbinsa don kada su samu matsala.