Gargadi ga azzalumi da tausar wanda ake zalunta (1)
Daga Hudubar Abdulmuhsin bin Muhammad Alkasim Masallacin Annabi, Madina Godiya da taslimi:Bayan haka, ku bi Allah da takawa ya bayin Allah! Matukar bin Sa da takawa, domin takawar Allah ita ce hanyar shiriya, kuma saba mata hanyar tabewa ce.Ya ku Musulmi! Allah Ya yi falala ga mutum kuma Ya karrama shi, kuma Ya saukaka masa […]
Daga Hudubar Abdulmuhsin bin Muhammad Alkasim
Masallacin Annabi, Madina
Godiya da taslimi:
Bayan haka, ku bi Allah da takawa ya bayin Allah! Matukar bin Sa da takawa, domin takawar Allah ita ce hanyar shiriya, kuma saba mata hanyar tabewa ce.
Ya ku Musulmi! Allah Ya yi falala ga mutum kuma Ya karrama shi, kuma Ya saukaka masa abubuwan natsuwa domin ya bauta maSa Shi kadai Madaukaki kamar yadda Ya yi umarni. Rayuwar mutane ba za ta daidaita ba, sai da addini, da shi ne suke samun sa’adar duniya da Lahira. Daga cikin addu’ar Annabi (SAW) akwai cewa: “Ya Ubangiji! Ka kyautata min addinina, wanda shi ne kariyar al’amarina. Kuma Ka kyautata min duniyata wadda abin rayuwata ke cikinta. Kuma Ka kyautata min Lahirata, wadda makomata ke cikinta.” Muslim ya ruwaito.
Asasin addini shi ne: adalci a cikin abin da ke tsakanin bayi da Ubangijinsu ta wajen kadaita Shi da bauta da kuma abin da ke tsakanin sauran halitta ta hanyar kauce wa yi wa juna ta’addanci. Domin zalunci shi ne asalin kowane sharri, kuma fasadi ne ga addini da rayuwar duniya. Allah Ya tsarkake kanSa daga zalunci kuma Ya sanya shi abin haramtawa a tsakanin bayi, inda Ya ce: “Ya ku bayiNa! Lallai Ni ne, Ni na haramta zalunci ga kaiNa, kuma Na sanya shi abin haramtawa a tsakaninku, don haka kada ku zalunci juna.” Musulim ya ruwaito. Abu Idris Alkhaulani (RH) maruwaicin wannan Hadisi ya kasance idan ya karanta wannan Hadisi sai ya gurfana a kan gwiwoyinsa.
Kuma Allah Ya ba da labari cewa ba Ya son azzalumi kuma Ya kore samun rabo daga gare shi, kuma Ya yi alkawarin karya shi, kuma ba wanda zai dauwama wajen taimakonsa. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka.” (k:2:170).
Maimakon haka Yana dora masa wani azzalumin da ya fi shi zalunci kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma kamar wancan ne Muke jibintar da sashin azzalumai ga sashi, saboda abin da suka kasance suna tarawa.” (k:6:129).
Ibnu Kasir (RH) ya ce: “Ma’ana muna dora sashinsu a kan sashi, Mu halaka sashinsu da sashi, Mu yi kamun ramuwa ga sashinsu da sashi, sakamako a kan zaluncinsu da ta’addancinsu.”
Kuma Allah Ya yi masa alkawari da mummunar makoma sai Ya ce: “Kuma wadanda suka yi zalunci, za su sani a wace majuya suke juyawa.” (k:26:227). Shuraihu (RH) ya ce: “Lallai azzalumi yana jirar ukuba ce, yayin da wanda aka zalunta yake jirar nasara (taimako).”
Azzalumi kwanakinsa a duniya ’yan kidayayyu ne, alhali Allah Yana yi masa talala ne. Allah Madaukaki Ya ce: “Saboda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Muna yi musu kidayar ajali ne kawai, kidayawa.” (k:19:84).
Duk wanda zaluncinsa ya tsawaita, karfinsa zai gushe, Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma da yawa Muka karya wata alkarya ta kasance mai zalunci, kuma Muka kaga halittar wadansu mutane na daban a bayanta.” (k:21:11). Ibnu kayyim (RH) ya ce: “Idan Allah Ya yi nufin Ya halaka makiyanSa, Ya wofantar da su, sai Ya bude musu hanyoyin da za su jawo wa kansu halakarsu da wofintarsu. Daga cikin manyansu a bayan kafirtarsu akwai: zaluncinsu da girman kansu da kaiwa karshe wajen cutar da waliyanSa da yakarsu da karkashe su da danne su.”
Allah Ya ambaci azzalumai a cikin LittafinSa da mummunar makomarsu, inda Ya ba da labari cewa lallai Shi Ya sanya su abin lura ne ga wasunsu. Fir’auna ya yi dagawa ya watsa fasadi a bayan kasa. Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne Fir’auna ya daukaka a cikin kasa, kuma ya sanya mutane kungiya-kungiya, yana raunanar da wata jama’a daga gare su; yana yayyanka ’ya’yansu maza kuma yana rayar da matan. Lallai shi, ya kasance daga cikin masu barna.” (k:28:4). Ya ma nuna girman kai ga Ubangiji inda ya musanta Shi, ya ce: “Ni ne ubangijinku mafi daukaka.” (k:79:24). Kuma ya yi alfahari da gudanar ruwa a karkashin kafafunsa har ya rika cewa: “Ashe mulkin Masar ba gare ni yake ba, kuma wadannan koguna suna gudana daga karkashina?” (k:43:51).
Duk irin wadannan abubuwa da ya rika yi, Allah Yana jiransa a madakata, Yana yi masa talala bai yi saurin kama shi ba, sai Ya gudanar da ruwa daga samansa Ya halaka shi da shi, Ya ce masa lokacin hallaka shi: “To a yau Muna kubutar da kai game da jikinka, domin ka kasance aya ga wadanda suke a bayanka.” (k:10:92). Sai Ya ba da labari cewa sarkafuwar igiyoyin ruwan kogi daga samansa a lokacin hallaka shi al’amari ne na wannan talala, sai Ya ce: “Saboda haka Allah Ya kama shi, domin azabar maganar karshe da ta farko. Lallai ne a cikin wannan hakika akwai abin kula ga wanda yake tsoron Allah.” (k:79:25-26).
Kuma Annabi Shu’aibu (AS) ya kira mutanensa zuwa ga Musulunci, kuma ya hane su daga zaluntar mutane, ya ce musu: “Ku cika mudu da sikeli da adalci, kuma kada ku nakasa wa mutane kayansu, kuma kada ku yi barna a cikin kasa kuna masu fasadi.” (k:11:85). Sai suka yi masa isgili suka ce: “”Shi ‘yar sallarka ce take umurtarka ga mu bar abin da ubanninmu suke bautawa, ko kuwa mu bar aikata abin da muke so da dukiyarmu? Lallai, hakika kai ne mai hakuri, shiryayye!” (k:11:87). Sai Allah Ya aika wuta a kansu ta kone su kuma ta kone dukiyarsu da suka tara da zalunci. Allah Madaukaki Ya ce: “Saboda haka, azabar ranar girgije ta kama su.” (k:26:189). Ma’ana wutar gobara wadda aka saukar musu daga sama. “Lallai ne ita (wutar) ta kasance azabar wuni mai girma.” (k:26:189).
Samudawa kuma baya ga shirka zunubinsu ya kasance soke dabbar gida ce da Allah Ya sanya musu a matsayin aya. Sai Allah Ya aika musu da tsawa ta kakkarya zukatansu. Shaihul Islam (RH) ya ce: “Duk wanda ya auka wa abubuwan da Allah Ya haramta, ya yi wasa da umarni da haninSa ya hallaka bayinsa ya zubar da jininsu, zai kasance mafi azabtuwa daga gare su.”
Idan tsanani da bala’i da bakin ciki da cutarwa suka auka wa muminai, to Allah Mai tausaswa ne a cikin kudurarSa, Mai hikima ne a cikin tadabburinSa, Mai iko ne a kan taimakon bayinSa, amma saboda hikimarSa ce Yake jarraba su. Allah Madaukaki Ya ce: “Wancan, da Allah Ya so, da Ya ci nasara a kansu, amma kuma (Ya yi haka ne) domin Ya jarraba sashinku a kan sashi.” (k:47:4).
Shi Madaukaki Mai karfi ne wajen kare bayinSa muminai. Allah Mai girman daraja Ya ce: “Lallai ne Allah Yana yin fada saboda wadanda suka yi imani.” (k:22:38). Ibnu Kasir (RH) ya ce: “Yana tunkude wa bayinsa da suka yi tawakkali a gare shi, suka koma gare shi, sharrin ashararai da kaidin fajirai, Ya kiyaye su, Ya kare su, Ya kuma taimake su.”
Wannan karewa ko tunkudewa ko yin fada tana aukuwa ne gwargwadon imanin bawa ga Maulansa. Wanda imaninsa ya karu, sai kariyar Allah ta yi karfi gare shi. kattada (RH) ya ce: “Wallahi Allah ba Ya tozarta duk mutumin da ya tsare addininSa.”
Musulmi yana riko ne da sabuban nasara da tunkude zalunci da danniya bisa kyakkyawar fata ga Allah, cewa lallai ne Allah zai taimake shi Ya ba shi nasara. Bisa i’itikadi da abin da kyawawan sunayenSa da siffofinSa Madaukaki suka nuna na karfi da Iko da Girma da Izza da kuma imani da abin da ya zo cikin Alkur’ani na alkawarinSa na taimakon muminai: “Kuma ya kasance tabbace, taimakon muminai wajibi ne a kanMu.” (k:30:47) da kuma yawaita ibada da istigifari da tuba zuwa ga Allah, saboda Allah Madaukaki Ya ce: “Idan kun taimaki Allah, Zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da duga-duganku.” (k:47:7). Sai kuma sikka kan cewa taimakon Allah yana kusa: “Lallai ne taimakon Allah yana kusa.” (k:2:214). Kuma ya yi yakinin cewa tawakkali ga Allah shi ne ginshikin samun taimako: “Idan Allah Ya taimake ku, to, babu marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya yarbe ku, to, wane ne wanda yake taimakonku bayanSa? Kuma ga Allah sai muminai su dogara.” (k:3160).
Kuma haduwar magana a kan gaskiya da watsi da rarrabuwa, karfi ne a kan makiya. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma kada ku yi jayayya har ku raunana, kuma iskarku (karfinku) ta tafi.” (k:8:46).