Gargadi ga azzalumi da tausar wanda ake zalunta (4)

Hakuri mabudi ne na fita daga kunci, kuma ana karfafa shi a lokacin aukuwar fitina da masifu. Kuma addu’a ce makami mafi karfi ta yakar abokan gaba ko adawa. Mai tsira da amincin Allah ya ce: “Ka ji tsoron addu’ar wanda aka zalunta, domin lallai ita babu hijabi a tsakaninta da Allah.” Muttafakun. Ibnu Akil […]

Gargadi ga azzalumi da tausar wanda ake zalunta (4)
Gargadi ga azzalumi da tausar wanda ake zalunta (4)

Hakuri mabudi ne na fita daga kunci, kuma ana karfafa shi a lokacin aukuwar fitina da masifu. Kuma addu’a ce makami mafi karfi ta yakar abokan gaba ko adawa. Mai tsira da amincin Allah ya ce: “Ka ji tsoron addu’ar wanda aka zalunta, domin lallai ita babu hijabi a tsakaninta da Allah.” Muttafakun. Ibnu Akil (RH) ya ce: “Ana amsa wa wanda aka zalunta cikin sauri.”

Kuma fa’alun Annabinmu (SAW) hakika shi ne an yake shi, an sanya masa takunkumi, an yi masa rauni, an cutar da shi, an yi masa makirci, an fitar da shi daga garinsa, an yi masa kaidi, an yi masa sammu, an yi masa sihiri. ’Ya’yansa shida sun rasu, amma ya kasance a cikin dukkan wadannan abubuwa yana cewa: “Fa’alu yana ba ni mamaki.” Sai aka tambaye shi kansa, sai ya ce: “Kalma dayyiba.” Muttafakun.
Musulmi mai yakini ne da samun taimakon Allah, kuma haramun ne a kansa ya karkata ga azzalumai. Allah Madaukaki Ya ce: “Kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci har wuta ta shafe ku.” (k:11:113). Kuma Allah bisa kudirarSa Yakan taimaki mai rauni koda tsanani ya yi masa daurin goro ko an wulakantar da shi. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Allah ne Marinjayi a kan al’amarinSa, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba.” (k:12:21).
Taimakon Allah ga muminai tana samuwa ne bisa imani da takawa, Shi Allah Madaukaki Mai taimakon bayinSa ne, koda adadinsu ko kayan fadarsu kadan ne, karfi dukkansa na Allah ne. Allah Madaukaki Ya ce: “Da yawa kungiya kadan ta rinjayi wata kungiya mai yawa da izinin Allah.” (k:2:249).
Kuma Shi Allah Madaukaki hakika Yana taimakon bayinSa ba tare da sun yi yaki ba, kamar yadda ya faru a Yakin Ahzabi. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Allah Ya mayar da wadanda suka kafirta da fushinsu, ba su samu wani alheri ba. Allah Ya isar wa muminai daga barin yaki, kuma Allah Ya kasance Mai karfi, Mabuwayi.” (k:33:25). Hakika Allah Ya taimake su ta hanyar jefa tsoro a zukatan makiya kamar yadda ya faru da Yahuduwan Bani Nadir, kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce: “Ba ku yi zaton suna fita ba, kuma sun tabbata cewa ganuwoyinsu masu tsare su ne daga Allah, sai Allah Ya je musu daga wajen da ba su yi zato ba, kuma Ya jefa tsoro a cikin zukatansu.” (k:59:2).
Kuma hakika Allah Ya aika rundunoni daga wurinSa domin hallaka masu ta’addanci. Abrahata ya zo da runduna daga Yemen domin rusa Ka’aba yana tafe da mafi karfin dabbobin daji wato giwa, sai Allah Ya dora mafi raunin dabbobi wato tsuntsaye a kansu, aka sanya kaidinsu a cikin bata.
To, idan kashe-kashe da yi wa Musulmi raunuka suka auku, kamar yadda suka faru a Uhudu, karshen al’amarin (samun nasara) nasu ne. Allah Madaukaki Ya ce: “Sai ka yi hakuri, lallai ne akiba (kyakkyawar karshe) tana ga masu takawa.” (k:11:49).
Bayan haka ya ku Musulmi! Wallahi idan aka kaskantar da Musulmi, to, su ne masu cin nasara, kuma idan aka yake su, to su ne masu samun galaba, idan aka kore su, su ne wadanda ake karfafawa. Wani bai taba ta’allaka da Allah ba a ce ya kaskanta, wani mutum bai nemi mafaka a wurinSa ba face ya samu taimako.
Ina neman tsarin Allah daga Shaidan jefaffe. “Kuma Muka yi nufin Mu yi kyauta ga wadanda ake raunanawa a cikin kasa, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su masu gadon kasa. Mu ba su iko a cikin kasa, kuma Mu nuna wa Fir’auna da Hamana da rundunoninsu abin da suka kasance suna saunarsa.” (k:kasas:5-6).
Allah Ya albarkace ni da ku cikin Alkur’ani Mai girma, kuma Ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da zikiri mai hikima. Ina fadin abin da kuke ji, ina mai neman gafarar Allah gare ni da ku da dukkan Musulmi, ku nemi gafararSa, lallai ne Shi Mai gafara ne, Mai jinkai.

Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah a bisa kyautatawarSa, shukura taSa ce a bisa datarwarSa da ni’imominSa. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a gare shi, girmamawa ga sha’aninSa. Kuma na shaida lallai Annabinmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da taslimi da sallamawa.
Ya ku Musulmi! Tarihi cike yake da wa’azozi da abubuwan lura, cike yake da abubuwan da suka faru da kissosi. Kuma a cikin sanin halayen al’ummomi da karshen zalunci da azzalumai akwai abin lura ga masu hankali. Mai rabo shi ne wanda ya wa’aztu da waninsa da labarin masu barna da karshen azzalumai. Karkacewar mujirimai abar lura ce ga wanda ya san Allah hakikanin saninSa, kuma ya yi imani cewa lallai Shi Mai iko ne a kan dukkan komai. Allah Mai girman daraja Ya ce: “Kowanne Mun kama shi da zunubinsa; daga cikinsu akwai wanda Muka aika a kansa da iska; daga cikinsu akwai wanda tsawa ta kama shi; daga cikinsu akwai wanda Muka kefe shi a cikin kasa; daga cikinsu akwai wanda Muka nutsar. Kuma Allah bai kasance Yana zaluntarsu ba, amma su ne suka kasance suna zaluntar kawunansu.” (k: Ankabuti:40).
karshen kowane azzalumi koda ta tsawaita mai zuwa ne, kuma nasara tana tare da hakuri, farin ciki na tare da bakin ciki, kuma tsanani sauki na biyo shi. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma lallai tsanani yana tare da sauki. Lallai tsanani yana tare da sauki.” (k:Sharh:5-6).
Sannan ku sani Allah Ya umarce ku da yin salati da taslimi a bisa AnnabinSa, cikin fadinSa: “Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.” (k:33:56).
Ya Ubangiji! Ka yi salati da taslimi a bisa bawanKa kuma ManzonKa Muhammad (SAW), ya Ubangiji! Ka yarda da Halifofin Annabi (SAW) hudu, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu da sauran sahabbai da tabi’ai da wadanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako da kuma mu don afuwarKa da karimcinKa da kyautatawarKa, ya mafi alherin Wanda Yake kawar da kai, Ya yi afuwa!
Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da Musulmi, Ka kare wuraren bayar da ilimin Musulunci, Ka darkake makiya addini da sauran masu girman kai da masu barna. Ka daidaita tsakanin zukatan Musulmi, Ka hada sahunsu, Ka gyara masu jagorantarsu. Ya Ubangiji! Ka hada kalmarsu a kan gaskiya ya Ubangijin talikai! Allah Ka taimaki addininKa da LittafinKa da Sunnar ManzonKa (SAW) da bayinKa Muminai, mujahidai na gaskiya.