Gargadi ga Larabawa
Edita idan har kasashen Larabawa kuka bude wa Amurka da kawayenta hanya suka shigo maku da sunan za su yaki ‘yan kungiyar Isis to za ku gane ba ku da wayau, domin duk kasar da Amurika da kawayenta suka shiga cikinta da sunan yaki da masu tada kayar baya, to zai yi mutukar wuya ka […]
Edita idan har kasashen Larabawa kuka bude wa Amurka da kawayenta hanya suka shigo maku da sunan za su yaki ‘yan kungiyar Isis to za ku gane ba ku da wayau, domin duk kasar da Amurika da kawayenta suka shiga cikinta da sunan yaki da masu tada kayar baya, to zai yi mutukar wuya ka ga kasar ta zauna lafiya. Don haka ina kira ga shugabannin kasashen Larabawa da ku yi watsi da kiran da Amurka da .Allah ya sa ku gane, amin. Daga Ababakar Lawal
Gidan Danmaye, a Jargaba, Bakori, Jihar Katsina +2348097627776
Soki burutsun shugabanni
Edita siyasar kasata Najeriya na tsaka mai wuya, ganin yadda shugabanni suka kasa yin komi game da abubawan cigaba, sai dai soki burutsu. Misali ga shi yanzu muna cikin lokacin damina, amma babu jihar da ta ta shi tsaye wajen nema wa talakkawa takin zamani. Kuma koda an kawo takin zamanin, za ka ga sai wadanda gwamnanti ke so a baiwa, su kuwa wadanda ba su da gata, sai dai su je kasuwa su saya, inda za ka ga shi ma wanda gwmnati ta bayar ne a raba, yan siyasa suka karkatar das hi. Ya ya za a yi harkar noma ta ci gaba a kasa? Daga Usman Adamu Aliero, Jihar Kebbi 07061594299
Ga dan Majalisar Bichi
Salam Aminiya ku mika godiyar al’ummar karamar Hukumar Bichi ga dan majalisa Lawan Shehu, bisa kokarin da yake yi mana wakilci mai cike da alheri. Daga shekara ta 2011 zuwa yau mun ga irin ci gaban da aka samu a mazabu 11 na karamar hukumarmu daga gwamnatin tarayya, ta fannoni daban-daban na kyautata zamantakewa. Daga Malam Abdu Saye, Bichi, Jihar Kano. 08091265624
A yi bincike
Bayyana sunayen Modu Shariff da Tsohon hafsan sojojin kasar nan Janar Ihejirike a matsayin masu tallafa wa kungiyar Boko Haram , abin a yi bincike a kai ne . Watakila siyasa ce kawai, don a bata musu suna, a kuma karkatar da hankulan yan Najeriya daga sha’anin boko haram . Ta yiwu kuma gaskiya ne suna da hannu . dan Adam ba shi da tabbas. Daga Mansoor Said PRP
07039215954 .
Sako ga al’umma
Edita ga sakona mnan zuwa ga ’yan uwa Musulmin Najeriya, mu ci gaba da addu’a a kasarmu da duniya baki daya. Allah Ya kawo mana zaman lafiya, ya ba mu shuabanni nagari, masu tausaya mana. Daga Yusif 07033412184.
Ga FM Jama’are
Edita ga sakon fatan alheri nan ga Manajan FM Jama’are, Alhaji Saminu Azare da jinjina da yabo kan namijin kokarin da yake yi wajen gudanar da aikinsa; bayana gaskiya da amana, ga shi da hakuri ga adalci. Daga Safiya 09033895572.
Haba Edita
Haba Edita ko kun gaji da mu ne? Na aiko sakon murna zuwa ga Gwmana Shema da amaryarsa Maryam ’Yar’aduwa ba ka saba. Na aiko ina fatan alheri ga shugabannin kananan hukumomin Jihar Katsina da suka yi nasarar zabe. Ba zan yi fushi ba, ina yi maka fatan alheri, tare da ma’aikatan Aminiya. Daga 08064932628.
Ga Hakimin Gezawa
Assalamu alaikum. Don Allah Edita ka mika min sakon gaisuwa ga Shugaban karamar Hukumar Gezawa, Alhaji Ibrahim Isa Jogana da mai girma Mai unguwar Mundubawa, Hakimin Gezawa, Alhaji Aminu Yusuf. Allah ya kara wa Haikimi lafiya. Amin. Daga Auwalu Kura G.M.W. Gezawa 08085200098.
Aminiya kotun talaka
An gaishe da kotun talakawan Najeriya. Masu tallar Ebola a Arewa, a yi taka tsantsan. Kun dai san yadda aka sha fama kan cutar Foliyo ko? To mai nufin al’umma da alheri Allah Ya tabbatar da nufinsa, wadanda kuwa nufinmu da sharri, don kawai su samu kudi, Allah ya mayar musu da aniyarsu. Amin. Allah Ya kare ku amin. Daga Sani Ya-Malam Kano 08126466663.
Ga ’yan majalisa
Salam. Bai kamata ’yan majalisa su yi shiru kan hukuncin da aka yanke wa sojoji 12 a daren Litinin, alhali an wanke wasu. Daga abubakar Lawan Fagge, Jihar Kano 08039129144.
Ga Gwamna Lamido
Aminiyar amana a mika min sakona ga Maigirma Alhaji Dokta Sule Lamido, gwamnan Jihar Jigawa, domin ya amsa kiran jama’a ya fito takarar shugaban kasar Najeriya, saboda kyawawan ayyuka da kake da tausayin jama’a da kishin kasa. Daga Hansa’u Hussaini Girbobo 07054956908.
Ga wakilin Hadejawa
Don Allah Edit aka b ani dama in isar da sakon godiya ga Hon Muhammad Bashir (Lawal Katta) dan takarr majalisar kasa, mai wakiltar Hadeja, a karkashin Jam’iyyar APC. Allah Ya ida nufi. Amin. Daga Yunusa Hamza (Gobenefa), Hadeja, Jihar Jigawa. 07030303626.
Fatan alheri a Aminiya
Don Allah Edita ka mika sakon fatan alheri ga dukkan jama’ar da ke tare da ku. Allah Ya kare ku daga sharrin duniya. Daga Jamilu Gambo Takai 08094571634/ 08166835313.
Mu yi rajista
Jama’ar Arewa mu tsaya mu yi rajista zabe mana. Hoton dan takara bas hi b ane mafita.. In muka yi wasa a zaben 2015 za a yi mana sakiyar da babu ruwa. Idan kunne ya ji, to jiki ya tsira. Daga Isa Dilwala, Abuja 08059044449
Wane ne Boko Haram?
A shekara ta 2012 Shugaba Jonathan ka ce ka san ko waye Boko Haram, ka ce a cikin gwamnatinka akwai boko haram; a cikin sojojinka. Sai gas hi yau an wayi gari, Tsohon Gwamnan Barno da Tsohon Hafsan sojojin kasa a mulkinka su ak zargi. Daga Isa sani Mai Arsenal 080725568447.
Ga Sarkin yakin Kazaure
Don Allah Aminiya a mia sakon fatan alheri g aMaigirma Sarkin Yakin Kazaure. Baba S. Aliyu bisa irin kokarin da yake yi wa musamman matasa, wajen taimaka musu a kan ahrkar karatu. Kazaurawa sun gaba dai, gaba dai har abada. Daga 07036056603.
Ga Aminiya
Salam Aminiya gaskiya ina jin dadin labaranku, musamman irin na ’yan fim din Hausa. Allah Ya kara hazaka da kwazo da imani. Nagode. Daga (H.r.a) 08035286002.
Babu ya Tata a Katsina
Duk yarfen masu yarfe Umaru Tata ya yi abin da ba wani dan siyasar day a taba kwatanta irin Tata a Katsina. Saboda haka al’ummar Katsina sun san wanda ya taimake su a zahiri. Daga NuraYakubu 09036330463.
Addu’a kan Ebola da Boko Haram
Edita ka taimaka mini in isar da sakon. Allah Ya kawo mana karshen Boko Haram da Ebola. Allah Ya ba Kwankwaso Najeriya; muna goyon bayansa dari bisa dari. Daga Babayaro Kyari, Kafin Hausa 08062297756.