Gargadi: Ya kamata masu halayyar son cin nama da kayan ciki su kula da irin naman da suke ci

DOKTA KIKIOPE OLUWARORE ta gudanar da wani kwarya-kwaryan bincike, inda ta gano yadda ake sayar da nama mai dauke da cututtuka daban-daban a kasuwannin Najeriya. Ga sakamakon binciken nata nan:   A bincikena, na taba samun wata anta tana baibaye da tsutsotsi, tana dauke da wata halitta da ke haddasa cutar Tarin Fuka. A kula, […]

Gargadi: Ya kamata masu halayyar son cin nama da kayan ciki su kula da irin naman da suke ci

DOKTA KIKIOPE OLUWARORE ta gudanar da wani kwarya-kwaryan bincike, inda ta gano yadda ake sayar da nama mai dauke da cututtuka daban-daban a kasuwannin Najeriya. Ga sakamakon binciken nata nan:

 

A bincikena, na taba samun wata anta tana baibaye da tsutsotsi, tana dauke da wata halitta da ke haddasa cutar Tarin Fuka. A kula, ta yiwu kana cin irin wadannan a matsayin namanka da kayan ciki.

Daga cikin wadannan cututtukan, kwayar cutar tsutsa da Tarin Fuka aka fi kamuwa da su a cututtukan da ke damfare a kayan ciki kuma an fi gane su cikin sauki a mayankar Najeriya da kasuwannin sayar da nama.

Najeriya kasar masu son cin nama ce. A daukacin sassa da al’adu da kabilu da kimar matsayi zamantakewar tattalin arziki, kusan kowane iyalai suna cin nama a kai-a kai a Najeriya. “Nama” na nufin sassan jikin nau’ukan dabbobi wadanda aka yanka don cin namansu, suna samar da nau’ukan abinci mai kara lafiya na ‘protein.’ Saboda bayar da fifiko da doka misali, mun bambanta nama bisa la’akari da irin jikin dabbar da aka ciro shi, wato irin su shanu da naman akuya da naman alade da sauransu.

Kayan ciki, wadanda a Yarbanci ake yi wa lakabi da ‘Inu-Eran’ na nufin sassan jikin dabba da ake iya ci tare da tsokar nama. Irin wadannan sassa sun hada da anta da koda da saifa da hanji da tumbi da zuciya da sauransu. Irin wadannan kayan ciki nau’ukan abinci mai dadi ne a wajen ’yan Najeriya masu cin nama, wadanda ke hada abinci da miya da romo da kayan ciki.

Yanzu saboda dalilan kariyar lafiya, yana da muhimmanci ga daukacin kamfanonin sarrafa kayan abinci ko cibiyoyi su kula da inganci da tsaftar wajen sarrafa kayan abinci kafin su sayar wa al’umma su ci. Dangane da tsokar nama da kayan ciki, mayanka da mahautan da ke aiki (ko sana’a) su ke da alhakin yankawa da sarrafawa da sayar wa al’umma nama su ci. Sai dai a wajen mafi yawan ’yan Najeriya, Abbatuwa ko Mayanka ba su da cikakkiyar kula da lafiya da tsafta, inda suke cikin wani irin yanayi da ke nuni da cewa nama da kayan cikin da suke samarwa na tattare da hadarin illata lafiyar al’umma. Wani mummunan tsarin rashin kula da lafiya shi ne, sayar da nama da kayan cikin da aka ga sun kamu da cuta ga al’umma, domin su ci. 

A mafi yawan irin wadannan al’amuran, idan dabba ta kamu da cuta ko rashin lafiya, alamun cutar za su iya bayyana a sassan jikin dabbar. Wadannan sassan sun hada da daukacin kayan ciki kamar yadda aka bayyana a sama, musamman ma hanji da huhu da anta da koda da zuciya. Alamun wadannan cututtuka na iya bayyana a wadannan sassan jiki kamar kwayar cutar “Tubercles” (kwayar cutar da ke haifar da Tarin Fuka), inda tsutsotsi masu rai da kwayayensu kan sauya launin sassan jiki.

Idan aka sayar da kayan ciki mai dauke da cuta a mayankar Najeriya, hadarin da ke tattare da shi a hakikanin gaskiya zai iya hawa jikin mutum idan ya ci naman kayan cikin. Kuma a kasa irin Najeriya, inda ba a ciki sa ido ba, wasu mahauta suna sayar da naman dabba mara lafiya, dauke da cuta ba tare da an tantance ba, inda cin wadannan kayan ciki ke tattare da hadarin cutar da lafiya. Cututtukan da za a iya kamuwa da su ta hanyar cin nama da kayan cikin dabba mai dauke da cuta sun hada da Tarin Fuka da bazuwar kwayoyin cuta irin su (Salmonellosis, Brucellosis, Athrad, Protozoan) da sauransu, wadanda ke haifar da rashin lafiya; har ma su halaka mutum.

Tsutsotsin Ciki:

Tsutsotsi, wasu kwayoyin cuta ne da ke illata mutum ta hanyar cinye sinadaran abincin da ya kamata su shiga jikin mutum, sai su zuke masa jini, sannan su lalata muhimman sassan kafofin jiki. Tsutsotsi kan far wa mutane da dabbobi, don haka daga jikin dabbobin za su iya shiga jikin mutane ta hanyar cin tsokar nama da kayan ciki. Lamarin ya danganta da irin tsutsar, domin kuwa tsutsotsi da kwayayensu kan bayyana a mafi yawan kafofin jiki (nama ko kayan ciki), amma an fi samun su a hanji da tumbi da anta da huhu da koda da zuciya. Misalan tsutsotsin ciki sun hada da masu mazauni a hanji da tumbi da masu bin jini (Tapeworms, Flukeworms da kuma Roundworms). Irin wadannan tsutsotsi suna da hadarin gaske ga mutane, musamman ga kananan yara da da mata masu juna biyu da mutanen da garkuwar jikinsu ba ta da karfi – al’amarin da ke haifar matsalolin da suka hada da ciwon ciki da zawo da amai da zama shakwal babu nauyi da tsomarewa (rashin girman jiki) da sankarar jini da kumburin fata da mutuwa. A matsanancin yanayi, sukan yadu a hanjin mutum, ta yadda za su toshe shi su haifar da babbar illa ga kayan cikin mutum da suka hada da zuciya da huhu da anta da kwakwalwa da koda – al’amarin da ka iya zama sanadin mutuwa.

Cututtukan tsutsa, boyayyun al’amura ne da ke tattare da dabbobin da ake yankawa a mahautun Najeriya, sai dai kuma namansu ana sayar da shi ga al’umma don su ci. Wasu tsutsotsin suna da girma yadda idanu za su iya ganinsu, inda suke fitowa daga jikin dabbar da aka yanka. Sauran nau’ukan tsutsotsin ba za a iya ganinsu a tsokar nama ko kayan ciki ba. daukacin wadannan al’amura dai na nuni da cewa da wuya a ga kwayayen tsutsotsin da ido. Don haka yana da muhimmanci a fahimci cewa kwayaye da tsutsotsin suka nasa don kyankyashewa na tattare da hadari, ta yadda za su iya girma su zama manya da sun shiga jikin mutane.

Huhu da anta masu dauke da kwayar cutar Tarin Fuka:

Ko ka taba shiga kasuwa don sayen kayan ciki (huhu ko anta)? Ko ka taba ganin huhu ya yi duhu-duhu da fari-fari da toka-toka barin gabansa ko ya kumbura ya bulluko ta waje? Sannan ko ka taba ganin mai sayar da naman, don ya ja ra’ayinka cewa naman na da kyau, sai ya yanki dan kadan ya sa a baki ya tauna? Ko kuma kana sha’awar cin kayan ciki, musamman huhu da zai ba ka damar taunawa kamar kana cin biskit ko cingam da za ka dade kana taunawa a baki?

Mutane da dama a kasar Yarbawa da ke Kudu Maso Yammacin Najeriya sun san abin da suke nufi da Fuku Elegusi, wato fankacecen huhu. Har ma an dauka nama ne mai dadin  gaske a wajen masu sayar da nama da masu ci, don har nuni ake yi da cewa “yana dadewa a baki ana tauna,” sabanin huhun da aka saba da shi, wanda ba ya dadewa ana taunawa saboda ba shi da gautsi kuma ga shi da gajarta. Saboda irin wannan fahimta ta sanya mahauta ke jan hankalin masu sayen nama da cewa “naman fankacece ne mai gautsi.”

Za mu kammala