Gargadin Hukumar NIHSA kan ambaliyar ruwa

Yan Najeriya da suke zaune a kusa da koguna a jihohin Kebbi da Sakkwato da Zamfara da Katsina da Neja an gargade su a kwanakin baya cewa su gaggauta kaura zuwa yankunan da suka dace a nesa da kogunan don kauce wa yiyuwar haduwa da ambaliyar ruwa da ake hasashen za ta auku daga watan […]

Gargadin Hukumar NIHSA kan ambaliyar ruwa
Gargadin Hukumar NIHSA kan ambaliyar ruwa

Yan Najeriya da suke zaune a kusa da koguna a jihohin Kebbi da Sakkwato da Zamfara da Katsina da Neja an gargade su a kwanakin baya cewa su gaggauta kaura zuwa yankunan da suka dace a nesa da kogunan don kauce wa yiyuwar haduwa da ambaliyar ruwa da ake hasashen za ta auku daga watan Yuli zuwa Satumban bana. Babban Daraktan Hukumar Kula da Yanayin Ruwa ta Kasa (NIHSA)  Injiniya Clement Nze, a wani taron da aka gudanar don wayar da kai kan barazanar ambaliyar ruwa da  hanyoyin kauce mata na shekarar 2019, ya nemi a gaggauta kwashe jama’ar da suke a zaune a yankunan da suke daf da kogunan da suke a jihohin da aka zayyana a sama.

Nze ya lissafa wasu yankuna da dama a Sakkwato wadanda suke kan gabar kogunan da suke fuskantar wannan barazana. Haka ma Zamfara ya bayyana Birnin Magaji da Kiyawa da Bakura da Bungudu da Shinkafi da Gusau da Kauran Namoda da kuma  Maradun a matsayin wurare mafiya fuskantar  hadarin ambaliyar ruwan. Ya kara da cewa a Jihar Neja al’ummar  Agwara da Magama suna cikin masu fuskantar barazanar, sannan  al’ummar Musawa a Jihar Katsina da wasu yankunan Katsinan ita kanta  ma suna daga cikin masu fuskantar barazanar ambaliyar ta bana.

Nze ya ce “Don haka muna kiran wadannan jihohi da abin ya shafa da kuma hukumomin da suke da alhaki su gaggauta dauke mazauna  gabar koguna da sauran jama’ar da suke gudanar da harkokinsu na rayuwa a kusa zuwa wasu wuraren. Haka kuma ya zama wajibi su yashe duk wasu hanyoyi da magudanan ruwa da suka toshe don ba ruwa damar wucewa kai-tsaye.”

Wannan gargadi na Hukumar NIHSA ya biyo bayan ambaliyar da aka samu ne a wasu yankuna na jihohin Arewa. A cikin wannan mako da muke ciki ne dai al’ummar Okpoko da ke Karamar Hukumar Ogbaru a Jihar Anambara sun fada cikin bala’in ambaliya wacce ta share kimanin gidaje 300 tare da raba kimanin mutum 2, 000 da muhallansu.

Ambaliyar ruwa dai kamar sauran bala’o’i tana aukuwa ce ba tare da ta bayar da wata babbar alama ko gargadi ba. Kuma tana faruwa ce idan aka samu karuwar ruwan sama wanda yake tilasta wa madatsun ruwa yin ambaliya zuwa cikin koramu da gulabe wadanda su kuma da zarar sun cika sun batse sai su yi ambaliya zuwa cikin gidajen mutane. A baya-bayan nan dai ambaliyar ruwa ta zama bala’in da ya fi kowane bala’i raba mutane da gidajensu. Sannan tana rusa gine-gine musamman ganin yadda babu kyakkyawan tsari na gine-gine a birane da karkara da kuma yawan karuwar jama’a da canjin yanayi da yadda mutane ke jibge shara a cikin magudanun ruwa wanda hakan kan taimaka wajen haifar da ambaliya.  Wannan gargardi dai wata alama ce da ta haska yadda ya zama wajibi wajen gwamnati ta samo wasu ingantattun hanyoyi na inganta yadda ake tsarawa da kuma gina muhalli. Sannan ya zama wajibi gwamnati ta samo wasu hanyoyi na zamani na auna yawan ruwan da suke a madatsun ruwa ta yadda za a iya samar da wata sahihiyar hanya ta yin gargadi ga jama’a. sannan a karfafa dokar da za ta hana yin gini daf da kogi da kuma gini a kan hanyoyin ruwa don a takaita barnar da take faruwa da zarar an samu ambaliya.  Haka a cikin gaggawa, ya kamata gwamnati ta samar da kwararrun ma’aikata da kayan aiki wadanda za su zauna cikin shirin ko-ta-kwana don duba yanayin yadda ruwa yake toroko a madatsun ruwa ta yadda za su iya rika budewa tare da rage ruwan. Sannan ya kamata gwamnati ta tanadi kayan agajin gaggawa da na jinkai wadanda suka hada da sutura da barguna da magunguna tare da samar da alluran rigakafi daga cututtukan da ka iya barkewa bayan aukuwar ambaliyar.

Su kuma a bangaren mazauna wadannan yankuna ya kamata su tashi tsaye su giggina hanyoyin ruwa a inda ake bukatar haka, sannan su yashe wadanda suka toshe. Sannan dai su rushe duk wani gini da yake a kan hanyar ruwa kuma yake kawo wa ruwan tarnaki wajen gudana.  Haka samar da wata taswira da ke nuna wuraren da suke fuskantar wannan barazana zai taimaka wa ma’aikatan Hukumar Ba da Tallafin Gaggawa ta Kasa su gudanar da ayyukansu cikin sauki.

Idan kuma har wannan ambaliya ta faru, matsalalolin da suka shafi na lafiya sun zama wajibi a duba su. Domin akwai yiwuwar za a samu barkewar cututtuka wadanda ake dauka daga shan gurbataccen ruwa, ba ma kamar yanzu da wasu yankuna na kasar nan suke ta fama da matsalar cutar amai da gudawa. Sannan kuma akwai matsalar rashin isasshen abinci wacce ita ma ka iya zama barazana ga wadanda abin zai shafa.

Ba shakka akwai bukatar gwamnati da sauran masu ruwa-da-tsaki su hada karfi da karfe don samo sahihiyar hanya ta tsara ginin birane da karkara don kauce wa barazanar ambaliya a nan gaba a Najeriya. A nan gaba kuma ya kamata gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi su rika hana yin gini a kan hanyoyin ruwa komai bukatar matsugunnan da ake fama da ita.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos