Gargadin Majalisar Musulmin Oyo ga Gwamna kan rusa gidan kangararru ya yi tasiri
Gargadin da Majalisar Musulmin Jihar Oyo (MUSCOYS) ta yi wa Gwamna Seyi Makinde na Jihar kwanakin baya kan umarnin da ya bayar na a rusa gidan kangararru a Ibadan ya yi tasiri, inda wata majiya mai tushe da ke kusa da ofishin Gwamnan ta shaida wa Aminiya cewa, “Gwamnati ta jingine wannan batu waje daya. […]
Gargadin da Majalisar Musulmin Jihar Oyo (MUSCOYS) ta yi wa Gwamna Seyi Makinde na Jihar kwanakin baya kan umarnin da ya bayar na a rusa gidan kangararru a Ibadan ya yi tasiri, inda wata majiya mai tushe da ke kusa da ofishin Gwamnan ta shaida wa Aminiya cewa, “Gwamnati ta jingine wannan batu waje daya. Babu batun rusa gidan a yanzu domin an riga an gurfanar da malamin da ya mallaki gidan wato Alfa Isma’il Olore a gaban kotu.”
Bayan bayar da belinsa Alfa Isma’il Olore, ya musanta zargin da ake yi masa kan rashin kula da lafiyar mutanen da ake tsare da su a cikin gidan da ke manne da Babban Masallacin Juma’a. “An ce a boye muke binne gawar mutanen da suka rasu a lokacin da suke tsare kuma an ce muna cin naman mutanen tare da wadansu abubuwa marasa kyau da aka danganta su da wannan gida. Wallahi babu kanshin gaskiya a cikin dukkan wadannan abubuwa da aka kirkiro domin bata mana suna. Duk mutanen da ka gani a cikin gidan nan iyayensu ne suka kawo su domin mu rika yi musu addu’o’i, a yi musu maganin ciwon da ke damunsu,” inji shi.
Kan batun daure mutane da sarka sai malamin ya ce “Hotunan da wasu kafofin labarai na Intanet suka watsa da sarka a kafafun mutane ba hotunan mutanen gidan nan ba ne. Ai kowa ya ganewa idanunsa a ranar da ’yan sanda suka shigo cikin gidan suka kwashe dukkan mutanen da muke tsare da su, babu wanda aka samu da igiya ko sarka ko wani abu a hannu ko kafarsa. Duk mutumin da zai fadi gaskiya to kuwa zai ce abun da ya gani a ranar babu wanda aka daure shi da sarka kamar yadda ake bata mana suna. Gaskiya ce a shekarun baya muna daure wadansu mutane a kafa amma yau shekara 11 ke nan da muka daina. Tun cikin shekarar 2008 muka daina haka kwata-kwata a nan gidan da muke jinyar mutane,” inji shi.
Da take bayani kan mutanen da aka kwashe daga gidan, Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a, Misis Abosede Abioye, ta ce tuni aka mika mutanen ga iyayensu na asali. Ta yi alkawarin yin adalci a kotun da aka gurfanar da malamin a gabanta.