Garin Agyaragu -Tasha a Nasarawa ba na Koro ba ne – Mai Unguwa
Mai magana da yawun Mai Unguwar Ayaragu-Tasha da ke karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Ahmed ya musanta ikirarin da ke cewa garin Agyaragu-Tasha na kabilar Koro ne kamar yadda Daraktan Gudanarwar Yankin, Mista Iliya Dagba ya bayyana wa jaridar Aminiya, kwanakin baya. Alhaji Ibrahim, a yayin martanin ga daraktan a madadin mai […]
Mai magana da yawun Mai Unguwar Ayaragu-Tasha da ke karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Ahmed ya musanta ikirarin da ke cewa garin Agyaragu-Tasha na kabilar Koro ne kamar yadda Daraktan Gudanarwar Yankin, Mista Iliya Dagba ya bayyana wa jaridar Aminiya, kwanakin baya. Alhaji Ibrahim, a yayin martanin ga daraktan a madadin mai unguwar na rikon kwarya, Alhaji Muhammadu Murtala, ya ce a tarihin garin baki daya ba a taba yin masarautar al’ummar Koro ba kuma babu wata unguwa da take ta Koro a garin Agyaragu-Tasha da ma sauran yankin baki daya. Ya kara da cewa bayan tsohon mai unguwar garin, marigayi Alhaji Jibrin Alhassan Nana ya rasu ne sai duk kabilun da ke yankin suka tattauna, inda suka amince a nada Alhaji Muhammadu Murtala wanda dan kabilar Rindire ne a matsayin mai unguwa na rikon kwarya; kafin a nada ainihin sarkin garin.
Ya kuma musanta maganar da Mista Iliya Dagba ya yi, cewa gwamnatin jihar ta amince cewa garin na Koro ne saboda haka suna da damar nada sarkinsu a duk lokacin da suka so, inda ya ce babu umarni ko bayani daga gwamnatin jihar da ya tabbatar da haka. Ya bayyana maganar da daraktan ya yi a matsayin abin da ka iya jawo rikici a yankin.
Haka kuma ya ce daraktan da ya yi wancan ikirari, yana nuna son kai a yayin dibar ma’aikatan gwamnati a yankin, inda a cewarsa yana so ne ya yi amfani da wannan dama wajen fifita al’ummar Koro, inda ake yin watsi da sauran kabilu da ke zaune a garin.
Daga nan sai ya yi kira ga al’ummar yankin su yi watsi da maganar daraktan, cewa garin na Koro ne. Ya kuma tabbatar da cewa masarautar za ta tabbatar da ta nada sarkin garin da zarar ta kammala tattaunawa da gwamnatin jihar, wanda a cewarsa ta sanar da ita bukatarsu ta nada sarkin garin don samun ci gaba mai ma’ana.
Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne ne Daraktan Gudanarwar yankin Agyaragu-Tasha, Mista Iliya Dagba ya bayyana wa Aminiya cewa garin na Koro ne kuma a cewarsa, gwamnatin jihar ta amince Korawan su nada sarkin garin a duk lokacin da suka ga dama.