Garin da ake saya wa birrai gonaki

Mutanen garin ne suke hidimar ciyar da wadannan birrai a kowane lokaci.

Garin da ake saya wa birrai gonaki

Birrai

An gano cewa mutanen wani kauye mai suna Upla a Jihar Maharashtra ta kasar Indiya saboda kimar da suke bai wa birrai sukan sayi gonaki da sunan birran.

Duk da cewa a kasar Indiya filin noma abu ne mai matukar daraja da ba a wasa da shi, amma saboda darajar da wadannan mutane suke bai wa birran sukan sayi gonaki da sunan birrai saboda karfafa darajarsu.

A yanzu an gano cewa, sama da eka 32 na gonaki a garin an saye su ne tare da yi masu rijista da sunayen birrai kamar yadda shugaban kauye ya tabbatar.

Har wa yau wadannan gonaki da aka saya domin birran, ma’aikatan lura da gandun daji na Ma’aikatar Noma da Kiwo ne ke da cikkkaken iko a kan gonakin, su ke da wuka da nama kansu, kuma za su iya shuka duk wani abu da suka ga ya dace domin amfanin birran.

Har wa yau, mutanen garin ne suke hidimar ciyar da wadannan birrai a kowane lokaci.

Birran a duk lokacin da suka ji yunwa sukan bi gidagida domin samun abin da za su ci daga mutanen garin.

Baya ga ciyar da birran da mutanen yankin ke yi har wa yau sukan ba su kyaututtuka a lokacin daurin aure ko wani biki kamar yadda jaridar Times of India ta ruwaito.

Sai dai a baya an samu labarin wani gungun birrai sama da 300 sun taba far wa garin da barna iri-iri, kama daga satar abinci da balle gidajen mutane har ma da kai wa mutanen garin hari duk lokacin da suka yi yunkurin korarsu.

Amma a yanzu ba a samun irin wannan ta’addanci daga birran wadanda suka zama ’yan gida tare da sabawa da jama’a.