Garin kwaki muke ci kawai na tsawan kwanaki 8- Yakubu

Wani da aka kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane mai suna Mista Yakubu Simeon, ya ce kullum garin kwaki kadai ake basu har na tsawan kwanaki takwas da suka yi a hannun masu garkuwa da mutane. Yakubu, ya kara da cewa wasu daga cikin mu da aka kama sun mutu. Ko a […]

Garin kwaki muke ci kawai na tsawan kwanaki 8- Yakubu

Wani da aka kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane mai suna Mista Yakubu Simeon, ya ce kullum garin kwaki kadai ake basu har na tsawan kwanaki takwas da suka yi a hannun masu garkuwa da mutane.

Yakubu, ya kara da cewa wasu daga cikin mu da aka kama sun mutu. Ko a makon da ya wuce Mataimakin Gwamnan Nasarawa Dakta Emmanuel Akabe, ya fada tarkon masu garkuwan inda ya rasa ’yan sanda uku da direbobi biyu a Karamar Hukumar Akwanga da ke jihar.

Bayan ayarin Mataimakin Gwamnan sun wuce sai suka kama wasu matafiya suka ka yi garkuwa da su. Yakubu, yace masu garkuwan sun umarce su da cewa duk wanda ya yi yunkurin tserewa to zai rasa ransa.