Garkuwa: An kara girke ‘yan sanda a hanyar Sakkwato zuwa Gusau

Hukumar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta kara girke jami’anta a hanyar Sakkwato zuwa Gusau saboda yawaitar garkuwa da mutane da ake yi. Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Sakkwato Murtala Mani ne ya bayyana wa majiyarmu. Mani, ya bukaci jama’a da su sanar da hukumar ‘yan sanda abubuwan da zai iya kawo barazana ga tsaron yankunan don […]

Garkuwa: An kara girke ‘yan sanda a hanyar Sakkwato zuwa Gusau

Hukumar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta kara girke jami’anta a hanyar Sakkwato zuwa Gusau saboda yawaitar garkuwa da mutane da ake yi.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Sakkwato Murtala Mani ne ya bayyana wa majiyarmu.

Mani, ya bukaci jama’a da su sanar da hukumar ‘yan sanda abubuwan da zai iya kawo barazana ga tsaron yankunan don saurin daukan matakan da suka dace.

Mani ya tabbatar da cewa, ‘yan sandan zasu kare matafiya dake zirgazirga a hanyoyin.