Garkuwa da dalibai mafiya muni 10 bayan na Chibok
Hare-haren 10 da ’yan bindiga aka kai aka sace dalibai sassan Najeriya
Shekaru takwas kenan cur da suka gabata da makayan Boko Haram suka kai hari makarantar sakandare da ke Chibok, Jihar Borno, inda suka yi garkuwa da daruruwan dalaibai ’yan mata.
Duk da dai wasu daga cikinsu sun kubuta, amma har yanzu kimanin dalibai 109 na hannun mayakan, yayin da wasu 16 daga cikinsu suka rasu.
Wasu daga cikin daliban da aka sako, sun komo gida ne ba a cikin hayyacinsu ba, wasun su ma dauke da ’ya’yan da suka hai fa wa ’yan kungiyar.
Tun bayan aukuwar lamarin a ranar 14 ga Afrilun 2014, sai matsalar garkuwa da dalibai ta zama ruwan dare, musamman ma a yankin Arewacin Najeriya.
Ga jerin lokatu 10 mafiya mutni da aka yi gagarkuwa da dalibai a Najeriya tun bayan sace ’Yan Matan Chibok.
1- Sakandaren Legas
Mahara da ba a san ko su wane be sun kutsa cikin makarantar Model College mallakin Gwamnatin Jihar Legas a unguwar Igbonla a yankin Epe suka yi awaon gaba da daliban 10 ’yan babban sakandare zuwa cikin daji a watan Mayun 2017.
Bayan sun tafi da daliban suka sako hudu daga cikinsu a kan hanya kafin su sanya ragowar shidan a cikin kwalekwalen zamani su yi awon gaba da su.
Kafin nan, a watan Oktoban 2016 an kai makamancin harin a makarantar, inda mahara suka sace dalibai hudu da wasu ma’aikata biyu.
Ana zargin kungiyar wasu ‘yan taratsi da suka addabi yankunan jihohin Ogun da Legas da ayyukan fashi da garkuwa da mutane ne dai suka sace daliban.
2- ’Yan Matan Dapchi:
Sace dalibai mata a makarantar Dapchi ya faru ne Fabrairun 2018, kuma shi ne irinsa na biyu da aka yi garkuwa da dalibai mata bayan ’yan matan Chibok.
Da asubahi mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari a makarantar mata ta Government Girls Science and Technical College, Dapchi, inda suka kwashi dalibai 107.
Dapchi gari ne da ke cikin Bulabulin a yankin Karamar Hukumar Bursari a Jihar Yobe.
Sai dai an sako daliban bayan wata guda da sace su in banda Leah Sharibu, bayan da aka biya ‘fansa mai tsoka’, amma Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ya ce an sako daliban ne ba tare da wani sharadi ko biyan kudi ba.
Bayanai sun nuna na ki sako Leah Sharibu ne saboda ta ki yarda ta sauya addininta na asali ta kama wani.
3- Makarantar Kankara:
A ranar Juma’a, 11 ga Disamban 2020, wani gungun ’yan bindiga karkashin jagorancin Auwalu Daudawa, suka kai hari a makarantar kwana ta Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara a Jihar Katsina suka yi garkuwa da daliba maza kimanin 300.
Bayanan mazauna yankin sun nuna ’yan bindigar sun shiga makarantar ne da misalin karfe 10:15 na dare tare da harbe dan sandan da ke gadi a kofar shiga makarantar.
Da farko dai ’yan bindigar sun soma shiga sashen da ma’aikata ke da zama ne inda suka yi garkuwa da wata mata kafin daga bisani suka runtuma dakin kwanan dalibai inda a nan suka kwashi dalibai da daman gaske.
Daga baya Auwalu Daudawa ya sako daliban, shi kuma bayan ya tuba daga baya ya kuma tayar da tubar aka kashe shi a wani kazamin fada a cikin daji.
4 – Daliban Islamiyya 80 a Dandume
A watan Fabrairun 2020 ’yan bindiga sun yi garkuwa da daliban Makarantar Islamaiyya ta Hizburrahim da ke kauyen Mahuta a Karamar Hukumar Dandume ta Jihar Katsina.
Daliban sun yi kicibus da ’yan bindiga ne a hanyarsu ta komawa gida daga wani taron Mauludi da aka gayyace makarantarsu a kauyen Unguwan Alkasim.
Sun yi karo da gungun bata-garin sun yi kai hari kauyen Danbaure inda suka yi garkuwa da wasu mutum hudu suka sace shanu 12, daga ganin daliban kuma suka kara da su suka yi cikin daji da su gaba daya.
Amma an auna arziki mazauna yankin sun tsgeunta wa makwabtansu abin da ya faru, inda suka yi ta maza suka fito ritsa ’yan bindigar kofar rago, aka ceto daliban da sauran mutanen da suka sace.
5- FGC Kagara
A watan Fabrairun 2021 mahara suka kutsa cikin Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Kagara a Jihar Neja suka yi awon gaba da dalibai 27 a dakunan kwanansu da malamai uku da iyalansu mutum 12.
Maharan sun kutsa cikin makarantar ce da misalin karfe 10 na dare, kimanin wata biyu bayan sace Daliban Kankara.
Daga baya suka saki daliban bayan tattaunawa da su da gwamnatin jihar ta yi, da taimakon fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi.
6- ’Yan Matan Jangebe
Sama da dalibai mata 300 na Makarantar Sakandaren Jangebe da ke Karamar Talata-Marafa ta Jihar Zamfara aka yi garkuwa da su bayan mahara sun far wa makarantar watan Fabrairun 2021.
Maharan sun shiga gidaden malamai da dakunan kwanan dalibai inda suka kwashi na kwasa suka yi cikin daji da su.
Wani dan sanda ya rasa ransa a wannan hari, kana aka sako daliban bayan wasu ’yan kwanaki.
7- Kwalejin Afaka:
A ranar 11 ga Maris 2021, ’yan bindiga sun kai hari a Kwalejin Aikin Gona ta Tarayya da ke Afaka a Jihar Kaduna suka sace dalibai kimanin su 30.
Sai dai na sako su bayan shafe sama da kwanaki 50 a hannun masu garkuwa da mutanen.
8- Jami’ar Greenfield
A Jihar Kadunan dai, ’yan bindiga sun kutsa cikin Jami’ar Greenfield suka yi garkwau da dalibai kimanin 20 da malamai biyu a ranar 20 ga watan Afrilun 2021.
Daga baya maharan sun kashe wasu daga cikin daliban, kafin daga bisani a yi nasarar kubutar sauran da suka rage a hannunsu a ranar 29 ga watan Mayu.
9- Islamiyyar Tegina:
Sai kuma Jihar Neja, inda a watan Mayun 2021 ’yan fashin daji suka kai mummunan hari garin Tegina suka kwashi dalibai kimanin 136 da malamai a makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko.
Haka nan, barayin sun yi garkuwa da wasu mazauna yankin da ba a tantance adadinsu ba ciki har da wani tsohon kansila.
An sako daliban daga baya ne bayan da suka shafe kusan wata uku a hannun masu garkuwa da su. An sako daliban ne ta Brinin Gwari a jihar Kaduna.
10- Bethel Baptist
’Yan fashin daji sun kutsa cikin makarantar Bethel Baptist da ke Damishi, Jihar Kaduna a ranar 5 ga Yuli, 2021 suka suka sace dalibai sama da 120.
An kubutar da daliban ne rukuni-rukuni gwargwadon yadda iyayensu suka iya hada kudin fansar da aka nema.
Sai dai har yanzu, akwai ragowar dalibai hudu a hannun ’yan bindigar wadanda ba a sako ba kuma wadanda kawo yanzu sun shafe kwanaki 284 a hannun maharan.
Matsalar satar dalibai
Wani rahoton da aka shirya don tunawa da ’yan matan na Chibok, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa, tsakanin Disamban 2020 da Oktoban bara dalibai 1,436 da malamai 17 ne aka sace a makarantu daban-daban a Najeriya walau ta dalilin Boko Haram ko kuma ’yan fashin daji.
A cewar rahoton, “Satar dalibai na baya-bayan da aka yi ya haifar da rufe makarantu na tsawon lokaci, kuma ya yi tasiri matuka wajen hana sa yara a makaranta da kuma kin zuwa makaranta a bangaren dalibai.
“Hakan ya kawo karuwar auren wuri da kuma daukar ciki a tsakanin yara mata dalibai.”
A wata sanarwa da ta fitar aranar Alhamis, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya nuna kimanin makarantu 11,536 ne suke rufe a Najeriya tun daga watan Disamban 2020 sakamakon matsalolin garkuwa da mutane da kuma rashin tsaro.
Tara kara da cewa rufe makarantun ya yi tasiri wajen haifar da cikas ga sha’anin karatun yara kimanin miliyan 1.3 a zangon karatu na 2020/2021.