Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya
Ba ni da wata masaniyar cewa an yi amfani da layin nawa wajen neman kuɗin fansa.
![Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2024/08/police.webp)
An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.
Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan wani mai suna Tasiu Abdullahi a ranar 20 ga watan Disamba.
- DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa
- An harbe ’yan sanda biyu a Yobe
Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi, Hashim ya bayyana cewa jami’an tsaron har gida suka je suka kama shi da cewa an yi amfani da lambar wayarsa wajen karɓar kuɗin fansar mutumin da aka kashe, wato Tasiu Abdullahi.
Hashim ya bayyana cewa tun a ranar 12 ga watan Disamba ya je sayen sabon layin wayar a wurin wani mai suna Usman Abdullahi kuma ya nemi a yi masa rajistarsa.
Sai dai mai rajistar layin ya nemi ya dawo wani lokacin saboda rashin sabis tare da neman ya taho da shaidar ɗan ƙasa ta NIN ta wani ɗan uwansa la’akari da ƙarancin shekarunsa.
“Hashim ya ce, “na dawo na ɗauki shaidar NIN ɗin yayana na koma wurin rajistar layin.
“Sai dai mai rajistar layin ya shaida min ana kan aikin nawa sannan ya aike ni sayen katin waya.
“Bayan na dawo ya [mai rajistar] ce min an kammala aiki kuma ya ba ni layin da aka yi min rajistar na kama gaba na.
“Ba ni da wata masaniyar cewa an yi amfani da layin nawa wajen neman kuɗin fansa kamar yadda jami’an tsaron suke iƙirari.”
A nasa jawabin, mai rajistar layin, Usman Abdullahi, ya ce yaron ya sayi sabon layin ne a wurinsa amma ya bai wa wasu abokansa layin an kammala rajistar.
Sai dai Abdullahi ya ce ba shi da masaniyar abin da abokan suka da layin da suka karɓa kafin dawo wa yaron kayansa.