Garkuwa da mutane: Gobara daga kogi! (1)
Ga dukan alamu matsalar garkuwa da mutane tana neman zama gobara daga kogi wadda Hausawa suke cewa maganinta Allah. Idan aka wayi gari ba ka ji an sace mutum an yi garkuwa da shi ana neman kudin fansa ba, to kai ne kawai abin bai shafa ba. Amma da za ka leka ko ka bincika […]
Ga dukan alamu matsalar garkuwa da mutane tana neman zama gobara daga kogi wadda Hausawa suke cewa maganinta Allah. Idan aka wayi gari ba ka ji an sace mutum an yi garkuwa da shi ana neman kudin fansa ba, to kai ne kawai abin bai shafa ba. Amma da za ka leka ko ka bincika za ka samu labarin an kama wani ko wadansu ana neman iyali da dangi su biya kudin fansa a kusan kowace wayewar garin Allah. Misali ko a ranar Talatar da ta gabata wani makwabcina ya ce an kama wani abokin aikinsu tare da mutum bakwai a tsakanin kauyen Katari da Rijana da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Matsalar wadda ta taso daga yankin jihohin Gabas wato jihohin Ibo ta gangara Kudu maso Kudu, yanzu ta samu gindin zama sosai a jihohin Arewa, musamman jihohin Arewa ta Yamma uku wato Zamfara da Katsina da Kaduna da jihohin Arewa ta Tsakiya, kamar Neja da Kogi da kuma wani bangare na Yankin Birnin Tarayya, Abuja, yakunan da suke da dazuzzuka masu cike da itatuwa da sunkuru.
Babban abin takaici shi ne wadanda aka fi zargi da aikata wannan muguwar ta’asa akasari sun fito ne daga al’ummar Fulani, wadanda suka saba rayuwa a cikin daji. Al’ummar Fulani da aka san ta da kunya da biyayya a baya, yanzu tana neman rasa wadannan kyawawan halaye. Wannan ne kuma tushen bala’in da ake ciki a yanzu.
Ba a rana daya ’ya’yan Fulani masu garkuwa da mutanen suka tsunduma cikin wannan muguwar harka ba. Sun faro ne daga satar shanun danginsu, musamman a dazuzzukan da ke tsakanin jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna, inda lamarin ya watsu zuwa kusan duk wuraren da Fulani suke kiwon shanu.
Daga baya lamarin ya bunkasa ya kasura ya koma ga satar mutane, sakamakon matakan da aka dauka na rajistar masu kai shanu zuwa kasuwanni da sauran hanyoyin dakile satar shanun.
Mutane da dama suna alakanta satar mutane ana yin garkuwa da su don a biya kudin fansa da yadda aka rika sace wa Fulanin shanu a baya wanda hakan ya jefa su talauci da rashin abin yi. Sai dai kuma idan aka bibiyi abubuwan da suke faruwa za a ga cewa ba wadannan ne dalilan fadawar matasan Fulani a wannan muguwar harka ba, sai dai a ce lalacewar tarbiyya da mugunta da kazamar hadama ta neman tara abin da duniya a dare daya da son sharholiya ne suke jawo aukuwar wannan muguwar harka.
Misali shekarun baya na taba zuwa kauyen Uduwa da ke kan hanyar Birnin Gwari a Jihar Kaduna domin binciko wani labari na wani makiyayi Bafulatani da ake zargi da kashe kanen wani da ya ba shi kiwon shanu.
Muna dawowa Kaduna a cikin mota sai zancen ya tashi, abin mamaki sai na ji wata Bafulatana ta ce: “Ai mu Fulani da ne muka yi kunya har ake cutarmu mu hakura, amma yanzu da muka fitsare, duk wata tsiya da shegantaka mu ne muke samun lamba wan!”
Ta kara da cewa: “Lokacin da mu Fulani muka shiga karuwanci sai da duk wata karuwa a kasar nan ta sallama mana. Yanzu ga shi a fagen fashi da makami mu ake tsoro tun daga nan Arewa har Kudu.”
Wannan lamari ya faru ne lokacin da garkuwa da mutane ba ta karaso Arewa ba, tana can Kudu ana jin ta jefi-jefi.
Lokacin da aka sace tsohon minista, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma tsohon dan takarar Shugaban Kasa a karkashin hadakar jam’iyyun APP/AD a zaben 1999, Cif Olu Falae, da aka ce Fulani ne suka yi, na rika cewa an raina mana wayo, yaushe Bafulatani zai je tsakiyar Yarbawa ya saci wannan babban mutum haka? Amma da jami’an tsaro suka kaddamar da bincike sai ga shi sun kama wani Bafulatani a otel a garin Kwantagora a Jihar Neja bisa zarginsa da hannu a garkuwa da Cif Olu Falae. Kuma abin takaici da aka yi masa tambayoyi, sai ya ce wai sun kama Falae ne don su samu kudin da za su yi shagali Sallah!
Haka lokacin da aka sace Sarkin Ubulu-Uku da ke Jihar Delta, Cif Edward Ofule III a shekarar 2016, kuma aka kashe shi bayan an karbi kudin fansa, babu wanda ya taba tunanin za a samu hannun Bafulatani a wannan aika-aika. Amma sai ga shi an kama wata Bafulatana da wayar marigayi Sarkin a Jihar Adamawa inda ta ce bazawarinta ne ya ba ta! Duk yadda za mu so mu kare al’ummar Fulani kan wannan ta’asa da take faruwa dole ne mu fito mu bayyana gaskiyar abubuwan da suke faruwa musamman na gazawar dattawan Fulani wajen kula da rayuwar matasan Fulani masu tasowa.
Kamar yadda na fadi ba talauci ne ummul haba’isin fadawar ’ya’yan Fulani cikin wannan muguwar harka ba, tabarbarewar tarbiyya da kokarin tara abin duniya da hadama ne suke ingiza ’ya’yan Fulani cikin wannan muguwar harka.
Misali wannan jarida ta taba buga wani labari na wata Bafulatana da aka sace mijinta da ’ya’yanta da ita kanta a lokuta daban-daban a Karamar Hukumar Tafa da ke Jihar Neja a shekarun baya. Bafulanatar ta ce da suka ga haka sai suka yi niyyar yin hijira zuwa Jihar Nasarawa. Amma suna cikin tafiya da shanunsu sai aka kira su a waya aka shaida musu cewa duk inda za je za a bi su.
Bafulatanar wadda take tallar nono a cikin birnin Abuja ta kasa boye takaicinta, inda bayan ta fadi abin da ke damunta wani babban ma’aikaci ya kira hedkwatar ’yan sandan Najeriya ya nuna musu bacin ransa kan yadda irin wannan lamari ke tafiya ba tare da ’yan sanda sun magance shi ba. An ce hedkwatar ’yan sandan sun kira babban ofishinsu na Minna suka nuna musu bacin ransu su ma, inda su kuma suka ce a tura matar ta je a wurinsu a Minna a wata ranar Lahadi. Abin mamaki tana zuwa aka ce in tana da lambobin da ake kiransu ta buga, kuma tana bugawa sai ga wayoyin sun amsa, ma’ana har an kamo wadanda ake zargin.
Bafulatanar ta ce, babban abin da ya ba ta mamaki, shi ne wadanda aka kamo din Fulani ne ’yan uwanta da ta sani kuma masu shanu wadanda idan suka hadu da ita a kasuwa har tsugunnawa a kasa suke yi suna gaishe ta!
Ke nan masu tunanin cewa talauci ne ko raba Fulani da dabbobinsu da barayin shanu suka yi ne ke jawo garkuwa da mutanen da wadansu Fulani ke yi don neman kudin fansa, wannan ya nuna ba haka ba ne.
Sannan akwai wani da aka kama a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna aka yi garkuwa da shi wanda ya ce, a lokacin da suke tsare a hannun wadanda suka kama su, sun lura suna musanyar masu kula da su a dajin, wadansu su je kiwo yau, wadansu su je gobe! Wannan ya nuna ba talauci ne ko rashin dabbobi ke haifar da wannan mugun al’amari a tsakanin al’ummar Fulani ba.
Kamar yadda na fadi a baya mugunta da kazamar hadama ta tara abin duniya ne ke haifar da wannan mugun aiki. Hadamar tara abin duniya kuwa ba ta tsaya ga al’ummar Fulani kadai ba, akasarin ’yan Najeriya babbar cutar da take damunmu ke nan. Wannan abu ne da kowannemu ya sani, mun tsiri wannan muguwar dabi’a ta mugunta da hadama ta yadda ba ma ga abincin da za mu ci ba ko dukiyar da za mu biya bukatunmu ba, ta kai ko tafiya muke a kan abubuwan hawa, sai mun nuna zalama da mugunta.
Misali mu lura da yadda muke a duk lokacin da muka doso wuraren duba motoci na soji ko ’yan sanda za a ga ba mu bin layi daya don isa wurin, sai dai a ga muna rige-rige muna kafa layuka uku zuwa hudu duk da mun san cewa a can gaba layi daya za mu koma kafin mu isa ga jami’an tsaron!