Garkuwa da mutane: ’Yan sanda sun cafke mutum 30 a Kaduna
Rundunar ta kuma cafke wasu mutum huɗu da ake zargi da safarar makamai, tare da ƙwato bindigogi guda biyar
‘Yan Sandan Najeriya
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce ta kama mutum 30 da ake zargi da aikata garkuwa da mutane tare da ƙwato makamai da motoci da aka sace a cikin watan Afrilun 2026.
Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Rabiu Muhammad, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kaduna, inda ya ce ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri ya taimaka wajen daƙile ayyukan ta’addanci a sassa daban-daban na jihar.
Ya ƙara da cewa rundunar ta kuma cafke wasu mutum huɗu da ake zargi da safarar makamai, tare da ƙwato bindigogi guda biyar ciki har da bindigar yaƙi da tarzoma, da kuma alburusai.
A cewarsa, an kama wasu mutum shida da ake zargi da satar motoci, inda aka ƙwato motoci huɗu da aka sace.
Muhammad ya bayyana cewa nasarorin da aka samu sun samo asali ne daga tsauraran matakan tsaro, sintiri na haɗin gwiwa da kuma hare-haren dabaru da aka mayar da hankali kan masu garkuwa da mutane, ’yan fashi da makami, masu safarar makamai da kuma masu satar motoci.
Da yake bayyana wasu muhimman ayyuka, shugaban ’yan sandan ya ce jami’ain rundunar sun yi artabu da wasu da ake zargi ’yan bindiga ne a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 16 ga Afrilu bayan samun sahihan bayanan sirri.
Ana zargin maharan sun tsere da raunukan harbin bindiga, inda suka jefar da wata bindiga ƙirar AK-47 da alburusai.
A wani lamarin kuma, rundunar ta ceto wani yaro mai shekara bakwai da aka yi garkuwa da shi a garin Anchau da ke Ƙaramar Hukumar Kubau.
Jami’an ’yan sanda sun bi sawun masu laifin har zuwa Ƙaramar Hukumar Soba, inda aka ceto yaron, sannan daga baya aka kama wani da ake zargi a Jihar Katsina.
“Wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma yana taimaka wa binciken da ake ci gaba da gudanarwa,” in ji kwamishinan.
Ya ce, haka kuma, rundunar ta samu nasarori wajen yaƙi da satar motoci, inda a ranar 5 ga Afrilu, jami’an bincike suka kama wani da ake zargi a Zariya tare da wata mota ƙirar Toyota Corolla da aka sace, sannan daga baya aka sake gano wata mota da ke da alaƙa da shi. Ƙarin bincike ya kuma kai ga kama abokin aikinsa a Jihar Kano.
Haka zalika, ’yan sanda sun tarwatsa wata ƙungiyar da ake zargi da satar motoci a yankin Mando, inda aka kama mutum uku tare da ƙwato wata mota marar rijista da ake zargin ta sata ce.
A wasu ayyuka daban, jami’ai sun ƙwato bindigar yaƙi da tarzoma da harsasai da wani da ake zargi ya jefar yayin tserewa a gadar sama ta Kawo.
An kuma kama wani tare da wata bindiga ƙirar AK-47 da aka ƙera a gida a yankin Kurmin Zaki.