Garuruwa masu dogaye da gajerun lokuta a lokacin azumi

Watan azumin Ramadan wata ne da mabiya addinin Musulunci ke azumtarsa. Tsawon lokacin azumin a  kullum kan fara ne daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana wato lokacin buda baki, wanda kuma yake kasancewa gajere ko mai tsawo idan aka kwatanta da yadda yake a yankuna daban-daban na fadin duniya. Wannan ya sa wasu masu azumin […]

Garuruwa masu dogaye da gajerun lokuta a lokacin azumi
Garuruwa masu dogaye da gajerun lokuta a lokacin azumi

Watan azumin Ramadan wata ne da mabiya addinin Musulunci ke azumtarsa. Tsawon lokacin azumin a  kullum kan fara ne daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana wato lokacin buda baki, wanda kuma yake kasancewa gajere ko mai tsawo idan aka kwatanta da yadda yake a yankuna daban-daban na fadin duniya.
Wannan ya sa wasu masu azumin kan kwashe lokaci kankani tsakanin Sahul da buda baki, wasu kuma lokacin kan kasance mai tsawo matuka. Misali Musulmin da ke zaune a birnin Reykjabik na kasar Iceland sun kammala Sahul ne a yau (Juma’a) da misalin karfe 2:25 na safe kuma suna sa ran yin buda baki ne da misalin karfe 11:16 na dare, lokacin da rana ta fadi a can. Wannan na nufin cewa suna kwashe kimanin sa’a 21 na azumi a kullum kafin su yi buda baki. Amma akasin haka ne  a birnin Buenos Aires na kasar Argentina, inda Musulmin da ke birnin suke yin azumin tsawon sa’a tara kawai a kullum, wanda kuma ya zo daidai da lokacin hunturu.  Hakazalika, azumin na zuwa da sauki sosai ga Musulmin da ke kasashen Australiya da New Zealand, inda suma suke kwashe kimanin sa’a tara kawai daga lokacin kammala Sahul zuwa na buda baki. Ga jaddawalin sunayen wasu birane daban-daban na duniya da kuma tsawon lokacin da mazauna can ke kwashewa daga fara azumi zuwa buda baki a kullum.