Garuruwan Gambouru da Ashigashiya sun fada hannun ’yan Boko Haram

Rahotanni daga Jihar Borno sun ce wasu ’yan bindiga da ake zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kame garin Ashigashiya da ke kusa da garin Gwoza, kwana biyu bayan sun kwace garin Gambouru Ngala da ke kusa da iyaka da kasar Kamaru.Tun a daren Litinin ne mazauna garin suka ce sun fara jin karar […]

Garuruwan Gambouru da Ashigashiya sun fada hannun ’yan Boko Haram
Garuruwan Gambouru da Ashigashiya sun fada hannun ’yan Boko Haram

Rahotanni daga Jihar Borno sun ce wasu ’yan bindiga da ake zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kame garin Ashigashiya da ke kusa da garin Gwoza, kwana biyu bayan sun kwace garin Gambouru Ngala da ke kusa da iyaka da kasar Kamaru.
Tun a daren Litinin ne mazauna garin suka ce sun fara jin karar harbe-harbe.
Cikin dare a ranar Lahadi zuwa sanyin safiyar Litinin ne ’yan kungiyar Boko Haram suka kai mummunan hari Gamboru Ngala, harin da ya haifar da ba ta kashi a tsakaninsu da sojoji, inda wasu sojoji 480, suka ketara kasar Kamaru.
Wani mazaunin Gambouru mai suna Mukhtar Aliyu Modu, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa “Mayakan Boko Haram sun shiga Gamboru Ngala da sanyin safiya dauke da manyan makamai kuma sun rufe idanunsu da rawuna suna kabbarori tare da bude wuta da bindigogi, a lokacin muna fitowa daga masallaci bayan Sallar Asuba. Sun ce mana mu shige gidajenmu mu kulle kofofi, ba sun zo su kashe mu ba ne, yau sun zo ne su karbe iko da garin daga hannun sojoji.”
Ya ce ba su kashe kowa ba kuma ba su kona kowane gini na gwamnati ko na mutane ba. Ya ce ’yan bindigar su raba kawunansu biyu kafin su shiga garin Gamboru, rukunin farko sun shiga garin sun tunkari barikin ’yan sanda da sansanin sojoji inda suka fafata har zuwa karfe 7:00 na safe, kuma a lokacin ne rukuni na biyu mai yawa ya bullo zuwa wurin da suke fafatawa dauke da miyagun makamai, suka ci karfin jami’an tsaron.
Wani da ba ya son a fadi sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa “Da farko jami’an tsaro ne suka samu galaba a kan maharani, amma zuwan rukuni na biyu ne al’amura suka canja bayan da jami’an tsaron suka karar da almabarusan da suke da su, kuma da suka ga ba su da wani zabi ne sai suka gudu zuwa kasar Kamaru.”
Ya ce ’yan bindigar sun lalata sansanin jami’an tsaron bayan jami’an tsaron sun gudu, kuma an yi asarar rayuka a tsakanin bangarorin biyu a karon battar da aka yi.
’Yan gudun hijira daga Gamboru Ngala na kwarara kauyukan kasahen Kamaru da Chadi da wasu wuraren a Arewacin Borno, yayin da garin Gamboru ya koma hannun ’yan bindigar.
Malam Kime wani magidanci a Gamboru ya shaida wa wakilinmu cewa “Maharan sunyi ta zagaya garin cikin dare kafin su shigo don kwace shi, kuma bayan kwace garin sun rika sintiri a kan Babura dauke da manyan makamai, amma ba su kashe fararen hula ba. Domin bayan lafawar abin mun fito muna ta diban ruwa suna ta kewayawa amma ba su
taba kowa ba, duk da cewa jirgin yaki ya zo ya jefa wani bkm a kan iyakar Najeriya da Kamaru kuma ya tafi, amma har yanzu ba mu sake ganin wani jirgi ya zo ba, amma gaskiya a yanzu muna zaune ne cikin tsoro da fargabar abin da zai je ya komo.”
Garin Gamboru shi ne hedikwatar karamar Hukumar Ngala, kungiyar Boko Haram ta yi ta kai masa hare-hare, na baya-bayan nan shi ne na ranar 5 ga Mayu bana da aka hallaka mutum 300 da kone motoci 200 da Babura 100 tare da kayra gadar da ta hada Gamboru da sassan Najeriya da kuma kasar Kamaru, wanda hakan yayi sanadin katse harkar kasuwanci a tsakanin Najeriya da Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano

’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi 

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya