Gasar Aminiya: An fara tace labarun ’yan takara
Alkalan farko sun fara tantancewa tare da tace dinbin labaran da suka shiga Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Aminiya ta bana, jim kadan da rufe gasar a ranar Larabar makon jiya. Kamar yadda Shugaban Kwamitin gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi ya bayyana, ya ce an samu adadin mutum 285 da suka shiga gasar. “Ansamu sakonni da […]
Alkalan farko sun fara tantancewa tare da tace dinbin labaran da suka shiga Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Aminiya ta bana, jim kadan da rufe gasar a ranar Larabar makon jiya.
Kamar yadda Shugaban Kwamitin gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi ya bayyana, ya ce an samu adadin mutum 285 da suka shiga gasar.
“Ansamu sakonni da suka amsa gayyatar shiga gasar har 285. Sai dai kamar kowace irin gasa, an samu rubabi da ba su bi matakan da aka ajiye ba.
“Daga tacewar da masu kula da gasar suka yi zuwa yanzu, an tantance labarai guda 235.
“Su ma ba duka ne suka daidaitu da dokoki da ka’idojin da aka saka ba”, inji Farfesan.
Ya ce a halin yanzu ana kokarin karkare tace dukkan labaran guda 235, domin a fitar da zababbu, wadanda alkalai na gaba za su zauna a kai.
“Yanzu za a fitar da labarai mafiya inganci, wadanda daga cikinsu ne za a fitar da guda 15 mafi cancanta.
“A cikin 15 din ne kuma za a tace guda uku da suka yi zarra a mataki na daya da na biyu da kuma na uku,” a cewar Shaihin malamin.
Ita dai wannan gasa, kamfanin Media Trust Limited Abuja, masu wallafa jaridun Aminiya da Daily Trust ne tare da hadin gwiwar kamfanonin Gandun Kalmomi da Open Arts, Kaduna suka shirya ta da nufin bunkasa adabin Hausa.