Gasar cin kofin Afirka na matasa: Gobe Najeriya za ta hadu da Aljeriya

A ci gaba da gasar cin kofin Afirka na matasa na ’yan kasa da shekara 23 (U-23) da yanzu haka ke gudana a Senegal, a gobe Asabar 5 ga Disamba ne  kungiyar kwallon kafa ta Najeriya da aka fi sani da Dream Team za ta kece raini da ta Aljeriya a wasa karo na uku.Najeriya […]

Gasar cin kofin Afirka na matasa: Gobe Najeriya za ta hadu da Aljeriya
Gasar cin kofin Afirka na matasa: Gobe Najeriya za ta hadu da Aljeriya

A ci gaba da gasar cin kofin Afirka na matasa na ’yan kasa da shekara 23 (U-23) da yanzu haka ke gudana a Senegal, a gobe Asabar 5 ga Disamba ne  kungiyar kwallon kafa ta Najeriya da aka fi sani da Dream Team za ta kece raini da ta Aljeriya a wasa karo na uku.
Najeriya dai ta hada maki hudu ne kawo yanzu bayan ta lallasa Mali da ci 3-2 a wasan farko sannan ta yi 2-2 da Masar a shekaranjiya Laraba.  Ita ma Aljeriya tana da maki hudu ne kuma ita ke saman tebur bayan ta yi kunnen doki 1-1 da Masar a wasan farko yayin da ta lallasa Mali a wasa na biyu a shekaranjiya Laraba.
Wasan zai yi zafi, don duk kungiyar da ta samun nasara a wasan ne za ta haye matakin kusa da na karshe (semi-fainal). Amma idan Aljeriya ce ta doke Najeriya sannan Masar kuma ta doke Mali, ko shakka babu an cire Najeriya daga gasar kenan.  Haka ma idan Najeriya ta yi kunnen doki sannan Masar ta samu nasara, to nan ma Najeriya tana cikin matsala, don dukkan kasashen uku Aljeriya da Najeriya da Masar za su hada maki biyar-biyar kenan sai dai a duba yawan kwallayen kafin a tantance na daya da na biyu a rukunin na “B”.
Don haka abu mafi kyau shi ne Najeriya ta yi kokarin ganin ta samu nasara a wasan don ta haye matakin semi-fainal ba tare da matsala ba.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa