Gasar cin kofin Champions League: PSG da Bayern Munich sun shiga tsaka mai wuya
A shekaranjiya Laraba ne kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa da kuma na Bayern Munich da ke Jamus suka shiga cikin tsaka mai wuya bayan sun sha kashi a wasannin da suka yi na kwata fainal. PSG dai ta sha kashi ne a wajen FC Barcelona a gida da ci 1-3 a wasan […]
A shekaranjiya Laraba ne kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa da kuma na Bayern Munich da ke Jamus suka shiga cikin tsaka mai wuya bayan sun sha kashi a wasannin da suka yi na kwata fainal.
PSG dai ta sha kashi ne a wajen FC Barcelona a gida da ci 1-3 a wasan farko matakin kwata-fainal yayin da ita kuma Bayern Munich ta sha kashi a wajen na FC Porto da ke Fotugal da ci 3-1.
A ranar Talata mai zuwa ne kungiyoyin za su sake haduwa a wasannin zagaye na biyu da hakan zai tantance kungiyoyin da za su haye matakin kusa da na karshe (semi-fainal) a gasar.
Yanzu kulob din PSG yana neman ya zura kwallaye uku da nema ne a ragar Barcelona kafin ya haye mataki na gaba a gasar, yayin da Bayern Munich kuma take neman kwallaye biyu babu da nema a ragar FC Porto muddin tana son hayewa mataki na gaba.
A washegarin Laraba ne kuma kulob din Atletico Madrid zai kai wa na Real Madrid ziyara a wasa zagaye na biyu, bayan sun tashi babu ci 0-0 a wasan farko yayin da a daya wasan kuma Jubentus na Italiya ce za ta kai wa Monaco na Faransa ziyara a wasa zagaye na biyu, bayan Jubentus din ta samu nasara a wasan farko da ci daya mai ban haushi.