Gasar cin kwallon kafa na mata: Yau ’yan matan Najeriya za su yi gumurzu da na Austireliya
A yau Juma’a 12 ga watan Yuni ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya da aka fi sani da Super Falcons za ta yi wasanta na biyu da Austireliya a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata da yanzu haka yake gudana a Kanada. Wasan zai gudana ne da […]
A yau Juma’a 12 ga watan Yuni ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya da aka fi sani da Super Falcons za ta yi wasanta na biyu da Austireliya a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata da yanzu haka yake gudana a Kanada. Wasan zai gudana ne da misalin karfe 10 na dare agogon Najeriya.
A wasan farko da Najeriya ta yi a ranar Litinin da ta wuce tsakaninta da kasar Suwidin, an tashi wasan ne da ci 3-3.
Najeriya ta yi kokari a wasan, ganin yadda tun a zagayen farko Suwidin ta zurara mata kwallaye biyu a raga amma bayan an dawo hutun rabin lokaci ne Najeriya ta fanshe cin da aka yi mata. Sannan bayan an kara mata na uku, ana dab da tashi ne kuma ta sake fanshe cin da aka yi mata da hakan ya sa aka tashi wasan ci 3 da 3.
Saboda haka a yau Juma’a ne Najeriya za ta yi wasa na biyu da Austireliya, kuma wasa ne da Najeriya take bukatar samun nasara don ganin ta kai bantenta. Saboda kawo yanzu Najeriya da Suwidin suna da maki dai-dai ne a rukunin D. Amurka ce take kan gaba bayan ta doke Austireliya a wasan farko da ci 3-1 da hakan ya sa ta hada maki uku kuma take saman tebur a rukunin na D. Yayin da Najeriya za ta hadu da Austireliya a yau, ita kuma Amurka za ta kece raini ne da Suwidin.