Gasar Damben Mota: Bahagon Ebola ya buge Bahagon Maitakwasara
An yi wasan ne a Gidan Damben Ali Zuma dake Dei-dei a Abuja ranar Lahadi.
Rabe Bahagon Ebola ya buge Bahagon Maitakwasara a wasan kusa da karshe a gasar damben mota da ke gudana a Abuja.
Wasan ya gudana ne a ranar Lahadi 31 ga watan Oktoba, 2021 a Gidan Damben Ali Zuma da ke Dei-dei a Abuja.
An yi wasan ne mako guda bayan bude gasar wadda ’yan dambe goma sha biyu ne suka shiga.