Gasar damben shekarar 2014 ta kankama a gidan damben Alaba Rago

An fara gudanar da gasar damben gargajiya na shekarar 2014 a gidan dambe na kasuwar Alaba Rago da ke Jihar Legas.Shugaban kwamitin shirya gasar, Alhaji Aminu Bature Kucere ya bayyana cewa sun gayyato ’yan dambe fitattu daga sassa da dama a Najeriya.Alhaji Aminu ya ce, “Mun tsara za a ba wanda ya zo na daya […]

Gasar damben shekarar 2014 ta kankama a gidan damben Alaba Rago
Gasar damben shekarar 2014 ta kankama a gidan damben Alaba Rago

Daga tsakiya sanye da hula shugaban kwamitin shirya wasan dambe na kwasuwar Alaba Rago, Alhaji Aminu Kucere ya dafa mashin din da aka sa don ba zakara na dayaAn fara gudanar da gasar damben gargajiya na shekarar 2014 a gidan dambe na kasuwar Alaba Rago da ke Jihar Legas.
Shugaban kwamitin shirya gasar, Alhaji Aminu Bature Kucere ya bayyana cewa sun gayyato ’yan dambe fitattu daga sassa da dama a Najeriya.
Alhaji Aminu ya ce, “Mun tsara za a ba wanda ya zo na daya sabon mashin; na biyu za a ba shi Naira dubu talatin; sannan na uku zai samu Naira dubu goma. Kuma  mun yi tsare-tsare da dama don tabbatar da cewa an gudanar da gasar lami lafiya ba tare da wani tashin hankali ba. Mun tanadi komai  da ake bukata. Kuma tuni  ’yan wasan suka hallara, inda aka fara gudanar da gasar ba tare da bata lokaci ba.   Za a yi kimanin wata guda ana gudanar da gasar”.
Ya cigaba da cewa, “Mun shirya gasar ne don mu bunkasa ala’adarmu ta gargajiya, sannan mu nishadantar da jama’a. Kuma mun shirya gasar ne don mu taimaka wa masu sana’ar damben, mu kara fito da su duniya ta san su”.
Ya ce kawo yanzu sun shafe kimanin shekaru 10 suna shirya gasar ba tare da an samu tashin hankali ba, kuma an kasa ’yan damben, bangaren Jamus da bangaren Kudu da kuma bangaren Guramada.