Gasar Firimiya: Arsenal ta ci Fulham 3-0 a wasan farko
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta lallasa Fulham da ci 3-0 a wasan farko na Gasar Firimiyar Ingila. Gabriel Magalhaes da Willian sun dauki hankalin jama’a a karawar ta ranar Asabar – wasansu na farko a kungiyar Arsenal. Jadawalin Gasar Firimiyar Ingila na Makon farko Messi ya koma filin atisaye na Barcelona Alexandre Lacazette ne […]
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta lallasa Fulham da ci 3-0 a wasan farko na Gasar Firimiyar Ingila.
Gabriel Magalhaes da Willian sun dauki hankalin jama’a a karawar ta ranar Asabar – wasansu na farko a kungiyar Arsenal.
Alexandre Lacazette ne ya zura wa Fulham kwallon farko sannan Gabriel Magalhaes ya kara musu kafin daga Pierre-Emerick Aubamayeng ya ci ta uku.
A wasan da Arsenal ta wujijjiga Fulham, tsohon dan wasan Chelsea, William ya taka rawa a dukkannin kwallayen da aka zura wa Fulham, wadda ta sha dakile Arsenal din daga haurawa mataki na gaba.