Gasar Firimiya: Gobe za a shawo ta tsakanin Liberpool da Arsenal
A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a yi wasa mai zafi a gasar rukunin Firimiya ta Ingila a tsakanin kulob din Liberpool da Arsenal. Wannan shi ne wasa na uku bayan da aka fara gasar ta bana makonni biyu da suka wuce. Kawo yanzu Liberpool ce take saman teburin gasar bayan ta […]
A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a yi wasa mai zafi a gasar rukunin Firimiya ta Ingila a tsakanin kulob din Liberpool da Arsenal.
Wannan shi ne wasa na uku bayan da aka fara gasar ta bana makonni biyu da suka wuce.
Kawo yanzu Liberpool ce take saman teburin gasar bayan ta hada maki 6 a wasa biyu kamar yadda ita ma Arsenal ta hada maki 6 a wasa biyu amma bambancin kwallaye ya sa Liberpool take saman tebur a gasar yayin da Arsenal take matsayi na biyu.
Wasan goben ya nuna kungiyoyin da ke saman teburi ne za su kece-raini a tsakaninsu, inda magoya bayan kungiyoyin biyu suke fatan kulob dinsu ya samu nasara a wasan.
Ana sa ran gidajen kallon kwallon kafa a Najeriya za su cika da masu sha’awar kwallo don ganin yadda wannan wasa zai kaya da misalin karfe 5:30 na yamma agogon Najeriya.
Jadawalin gasar ya nuna cewa da misalin karfe 3:00 na yamma kulob din Manchester United zai karbi bakuncin kulob din Crystal Palace yayin da a jibi Lahadi kuma kulob din Bournemouth zai karbi bakuncin Manchester City da misalin karfe 2:00 na rana agogon Najeriya.
Idan za a tuna kulob din Manchester City ne ya lashe gasar a bara yayin da Liberpool ya kasance na biyu. Arsenal ce ta biyar yayin da Manchester United ta zama ta shida.