Gasar Firimiya:  Jibi Arsenal za ta hadu da Tottenham

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni ta Ingila ta Firimiya a jibi Lahadi kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta hadu da takwararta ta Tottenham a wasa karo na hudu.  Wasan zai gudana ne da misalin karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya a filin wasan Arsenal na Emirate Stadium. Dukkan kungiyoyin biyu suna […]

Gasar Firimiya:  Jibi Arsenal za ta hadu da Tottenham

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni ta Ingila ta Firimiya a jibi Lahadi kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta hadu da takwararta ta Tottenham a wasa karo na hudu.  Wasan zai gudana ne da misalin karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya a filin wasan Arsenal na Emirate Stadium.

Dukkan kungiyoyin biyu suna zaune ne a birnin Landan inda za su buga wasan da ake wa lakabi da Karon Battar Birnin Landan.

Kawo yanzu Arsenal ce take matsayi na uku a teburin gasar da maki 6 a wasanni uku.  Ke nan ta yi nasara a wasanni biyu, sannan an doke ta a wasa daya.

A bangaren Tottenham kuwa, ita ce ta bakwai a teburin gasar da maki hudu.  Ta yi nasara a wasa daya, ta yi canjaras a wasa daya sannan ta yi rashin nasara a wasa daya.

Zuwa wannan lokaci kulob din Liberpool ne yake jan ragamar gasar da maki 9 a wasanni uku, sai kulob din Man. City ke biye da maki 7 sai Arsenal mai maki 6 sai Leicester City ita mai maki 6 amma bambancin yawan kwallaye ne ya raba ta da Arsenal.

Wasannin za a buga a gobe Asabar sun hada da na Southampton da Manchester United, sai Chelsea da Sheffield United da Manchester City kuma da Brighton and Hobe Albion.