Gasar firimiya ta Najeriya: Kallo ya koma kasa
A ranar Lahadin makon jiya ne kulob din Enyimba da ke garin Aba a Jihar Abiya ya lashe kofin gasar firimiya bayan ya yi kunnen doki da kulob din Warri Wolbes a garin Aba. Maki 1 da kulob din Enyimba ya samu ne ya ba shi damar lashe gasar firimiya a karo na 7. Sai […]
A ranar Lahadin makon jiya ne kulob din Enyimba da ke garin Aba a Jihar Abiya ya lashe kofin gasar firimiya bayan ya yi kunnen doki da kulob din Warri Wolbes a garin Aba. Maki 1 da kulob din Enyimba ya samu ne ya ba shi damar lashe gasar firimiya a karo na 7.
Sai dai a yanzu da za a buga wasan karshe a jibi Lahadi, to hankalin kulob din da ke kasan teburin gasar a tashe yake, kasancewar wasan karshen ne zai tabbatar da ko wadansu daga cikin kulob-kulob din za su ci gaba da buga gasar a badi ko su koma buga gasar Nationwide.
Kulob din Bayelsa United a matsayi na 20 da maki 34 a wasa 37 da kulob din Taraba a matsayi na 19 da maki 37 a wasa 37 da kulob din Kwara United a matsayi na 18 da maki 39 a wasa 37 tuni sun san matsayinsu, domin ba za a ci gaba da buga gasar da su a badi ba.
Bayan an kammala gasar firimiya a Najeriya kulob 4 a karshen teburi su ne suke koma wa gasar Nationwide, don haka a yanzu saura kulob daya ya rage don a samu cikon kulob 4 da za su koma buga gasar Nationwide a badi.
Kulob din Elkanemi Warriors na Jihar Barno a matsayi na 12 da maki 49 a wasa 37 ya tsallake siradi, inda ko ya yi rashin nasara a wasan karshe ba shi da wata damuwa.
A yanzu da ya rage saura wasa daya a kammala gasar kowane daga cikin kulob biyar da suka hada da Lobi Stars a matsayi na 13 da maki 46 a wasa 37 da Rangers International a matsayi na 14 da maki 46 a wasa 37 da Sharks FC a matsayi na 15 da maki 45 a wasa 37 da Dolphins a matsayi na 16 da maki 44 a wasa 37 da kuma Akwa United a matsayi na 17 da maki 44 zai iya zama cikamakin kulob 4 da za su koma buga gasar Nationwide.
Wasan da zai fi daukar hankali shi ne tsakanin Akwa United da Lobi Stars, inda za a buga wasan a garin Akwa-Ibom, wadannan kulob din suna fuskantar barazanar koma wa buga gasar Nationwide, don haka wasa ne da gida ba zai yi tasiri ba, sai dai kowa karfinsa ya kwace shi.
Masu sharhi suna ganin kamar wasan da za a buga tsakanin Rangers International da Bayelsa ba zai yi zafi ba, kasancewar za a buga wasan a gidan Rangers ne, sannan Bayelsa United da ke matsayi na 20, tuni ya san matsayinsa, don haka ’yan wasansa ba za su zage damtse don nuna kwazo a wasan ba.
Kulob din Dolphins zai buga wasa a gidan Shooting Stars, wasan da idan Shooting Stars ya samu nasara zai tashi daga matsayi na 9 zuwa na 7, wanda hakan ba karamin kudi zai samu daga hukomomin da suka dauki nauyin gasar firimiya ba, dalili kuwa shi ne, matsayin da kulob bayan an kammala gasar shi ne yawan kudin da zai samu.
Sharks zai je wa Abia Warriors da ke garin Aba a Jihar Abiya, wasan da idan kulob din Abia Warriors ya samu nasara zai tashi daga matsayi na 10 zuwa na 8, inda hakan zai kara masa kudin da zai samu daga hukumomin da suka shirya gasar.
A yanzu dai da za a buga wasan karshe a jibi Lahadi ido ya koma kan kulob din Lobi Stars da Rangers International da Sharks da Dolphins da kuma Akwa United, don a samu kulob na hudu da zai koma buga gasar Nationwide bayan kulob din Bayelsa United da Taraba FC da kuma Kwara United sun san matsayinsu.