Gasar Hoto ta Daily Trust/Aminiya: Sharuddan shiga
Bayanin ka’idojojin shiga gasar daukar hoto don matasa.
A karon farko kafar yada labarai ta Daily Trust da Aminiya ta bullo da gasar daukar hoto na wata-wata domin matasa.
Ku shiga gasar daukar hoto ta Daily Trust/Aminiya ta hanyar daukar hotuna masu kayatarwa ku aiko mana domin samun kyautar data a kowane wata.
A wannan wata (Nuwamba, 2021) taken gasar shi ne ‘Mutumin Najeriya,’ ganin cewa ranar 19 ga Nuwamba ta kowacce shekara ita ce Ranar Maza ta Duniya.
Saboda haka, sai ku aiko mana da hotuna da ke nuna gwagwarmaya, nasarori da kalubalen da maza ke fuskanta a Najeriya.
Za a rufe shiga gasar ta wannan karon a ranar 17 ga Nuwamba, 2021.
Sharuddan shiga gasar:
1. Wajibi ne duk hoton da za a turo ya kasance na asali, sannan wanda ya aiko da shi ne ya dauki hoton.
2. Wajibi ne hoton ya kasance ba a taba amfani da shi a wata kafa ba.
3. Dole duk wanda zai shiga gasar ya kasance shekarunsa akalla 15.
4. A aiko da cikakken suna da adireshin mai shiga gasar tare da duk hotunan da aka turo.
5. Yawan hotunan da mutum daya zai iya shiga gasar da su ba zai wuce biyu ba.
6. Duk wanda ya turo hoto, to ya amince wa Daily Trust/Aminiya ta yi amfani da shi a duk kafofinta ba tare da kaidi ba.
7. A aiko da hotunan shiga gasar ta WhatsApp zuwa 0913 893 3390.
8. Daily Trust na da hakkin yin sauye-sauye ga wadannan sharuddan a kowane lokaci.
9. Duk hukuncin da kwamitin alkalan gasar ya yanke shi ne na karshe.
Allah ba mai rabo sa’a.