Gasar karatu

Wasu samari ne su uku suke gasar neman auren diyar limamin garinsu, sai rannan suka dunguma gaba daya suka tafi wurin surukin nasu, suka shaida masa bukatarsu.Liman ya tambayi saurayi na farko: “Yaya sunanka?” Ya amsa masa da cewa Ibrahim. “To karanta mana Suratul Ibrahim,” inji liman. Shi kuwa ya karanta sosai ba gargada. Da […]

Gasar karatu
Gasar karatu

Wasu samari ne su uku suke gasar neman auren diyar limamin garinsu, sai rannan suka dunguma gaba daya suka tafi wurin surukin nasu, suka shaida masa bukatarsu.
Liman ya tambayi saurayi na farko: “Yaya sunanka?” Ya amsa masa da cewa Ibrahim. “To karanta mana Suratul Ibrahim,” inji liman. Shi kuwa ya karanta sosai ba gargada. Da ya tambayi sunan saurayi na biyu sai ya amsa masa da cewa Yusuf. Don haka sai liman ya ce ya karanta Suratul Yusuf. Shi ma kamar na farkon ya karanta sosai cikin gwaninta. Da aka tambayi saurayi na uku sunansa, sai ya fara inda-inda: “Sunana Yasin, amma a gida iyayena suna kira na da kulhuwa.” (Shi a wayonsa, yana son liman ya ce ya karanta kulhuwallahu Ahad ne, domin kuwa bai haddace Suratul Yasin ba).